An Gudanar Da Taron Warware Matsalar Palastinawa A Birnin Paris

  • Lambar Labari†: 805311
  • Taska : Pars Today
Brief

An kammala taron tattaunawa kan matsalar Palasdinawa a birnin Paris na kasar faransa ba tare da cimma wani abin a zo a gani ba.

Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta bayyana cewa an kammala taron na Paris ba tare da halattar wadanda abin ya shafa kai tsaye ba, wato HKI da kuma gwamnatin cin gashin kai na Palasdinawa.

Gwamnatin kasar Faransa ta gabatar da shawarar farfado da tattaunawa tsakanin Palasdinawa da HKI a shekarar da ta gabata, sannan an gudanar da taron farko ne a cikin watan Jenerun shekara ta 2016 da ta gabata shi ma ba tare da wakilan HKI da kuma Palasdinawna sun halarci shi ba.

A wannan karon ma an fara taron a ranar 15 ga watan Jeneru da muke cikin sannan wani abinda za'a ce taron ya cimma shi ne yin All.. wadai da ci gaba da gine ginen da HKi take yi a lardunan Palasdfinawa da ta kwace kamar yadda kudurin majalisar dinkinduniya na 2334 ya bukata.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky