Gwamnatin Kasar Turkia Ta Bukaci Tsagaita Bude Wuta A Duk Fadin Kasar Syria

  • Lambar Labari†: 800210
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Gwamnatin kasar Turkia ta bukaci tsagaita bude wuta tsakanin sojojin kasar Siria ta kawayensu da kuma yan ta'adda a duk fadin kasar.

Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Turkia Mevlut Cavusoglu yana fadar haka a wani taron da  kasashen da suke goyon bayan yan ta'adda a kasar Siria suke gudanarwa a birnin Jadda na kasar Saudia.

Ministan yana fadar haka ne bayan da sojojin siria da kawayenta suka fatattaki yan ta'adda daga birnin Halab na kasar ta Siria a ranar Alhamis da ta gabata, sannan sun sha alkawarin cewa zasu ci gaba da fatattakan yan ta'addan a sauran yankunan kasar Siria da suke rika ta har zuwa kubutar da dukkan yankunan kasar daga hannun yan ta'adda.

Kasashe masu goyon yan ta'adda a yankin, wadanda suka hada ita Turkia, saudia da kuma wasu kasashen yankin  suna gudanar da taron gaggawa a kasar Saudai tun tattauna matakan da zasu dauka bayan sha kaye a kokarinsu na sauke shugaba kasar Siria Bashar al-asad da karbin bingida.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky