Amurka Za Ta Aika Karin Kwararun Sojoji Zuwa Syria

  • Lambar Labari†: 749795
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Nan gaba, a wannan Litinin ce ake sa ran shugaban Amurka Barack Obama, zai sanar da tura wasu karin kwararun sojojin kasar sa 250 a Syria.

Wani babban jami'in Amurka da bai so a bayana sunan sa ba, ya shaida cewa Obama zai tabbatar da hakan a wani jawabi da zai yi a birnin Hanova dake arewacin Jamus a ci gaba da ziyarar sa ta kwanaki biyu a kasar.

Majiyar ta kara da cewa babban aikin sojojin Amurkar shi ne, bada shawara da horo da kuma taimakawa 'yan tawaye Syria da kuma sojojin Iraki dana Syria dake yaki da 'yan ta'adan (ESIL).

kafin hakan dama Obama ya nuna matukar damuwar sa danganeda halin da ake ciki a Syria, inda ya roki bangarorin da ke rikici da juna a Syria da su maido da yarjejeniyar tsagaita musayar wuta da suka cimma a kwanan baya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky