Amurka da Rasha Sun Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Siriya

  • Lambar Labari†: 736545
  • Taska : HAUSA.IR
Brief

Saidai Yarjejeniyar ba ta shafi mayakan da ke da’awar jihadi ba a kasar ta Syria.

Kasashen Amurka da Rasha sun sanar da cimma yarjejeniyyar tsagaita wuta tsakanin bangaren gwamnatin Bashar Al Assad da kuma ‘yan adawa kasar.

Wannan yarjejeniyar za ta soma aiki ne daga ranar 27 ga watan Fabrairu nan daga bakin karfe 12 na dare agogo Siriya a cewar sanarwar.

Sai dai yarjejeniyar ba ta shafi mayakan da ke da’awar jihadi ba a kasar ta Syria da suka hada da 'yan ta'adan (IS).

Tuni Sakataren MDD Ban Ki-moon ya yaba da yarjejeniyar tare da yin kira ga bangarorin da ke rikici su amince da kuma yin aiki da yarjejeniyar don kawo karshen rikicin shekaru biyar daya daidaita kasar tare da lashe rayukan dubban mutane, tare da tursasawa Miliyoyi tserewa daga kasar.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky