Za a Ci Gaba Da Aiwatar da Takunkumi Kan Rasha-Nuland

  • Lambar Labari†: 710546
  • Taska : voahausa.com
Brief

Wata babbar jami’ar diplomasiyar Amurka tace za a ci gaba da aiwatar da takunkumin da aka kakabawa Rasha sabili da rawar da ta taka a rikicin kasar Ukrain har zuwa lokacin da zata mutunta yarjejeniyar da aka cimma. Mataimakiyar sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka Victoria Nuland ta kuma yi gargadi jiya asabar cewa, Moscow zata fuskanci takunkumi da suka fi na yanzu tsauri idan ta sake keta yarjejeniyar.

Nuland ta bayyana haka ne a Kyiv babban birnin kasar Ukraine, a wajen wani taron jami’an siyasa da kuma ‘yan kasuwa na kasashen ketare.

Tace idan aka aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a Minsk baki daya, da ta hada da mutunta diyaucin Ukraine da ya shafi kan iyakarta, daga nan zamu fara janye wadansu takunkumin.

Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai suna zargin Moscow da goyon bayan ‘yan ta’awaye masu ra’ayin Rasha da suka shafe watanni goma sha bakwai suna tada kayar baya a gabashin kasar Ukrain, suka kuma kakabawa Rasha takunkumi da dama da nufin hanata bada tallafin soji da kuma wadansu gudummuwa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky