Britania Ba Zata Amincewa Trump Ya Yi Jawabi A Cikin Majalisar kasar ba

  • Lambar Labari†: 810034
  • Taska : Pars Today
Brief

Shugaba majalisar dokoki kasar Britani John Bercow ya bayyana rashin amincewarsa da jawabin shugaban kasar Amurka Donal Trump a cikin majalisar dokokin kasar idan ya kawo ziyara a tsakiyar shekarar da muke ciki a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto John Bercow yan afadar haka a majalisar dokokin kasar ta Britania a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa tun kafin donal Trump ya bada umurnin hana mutanen kasashen musulmi 7 shiga kasar Amurka ba ya goyon bayan jawabinsa a majalisar, banlanta ya fitar da wadan nan dokoki na hana baki yan gudun hijira shiga kasar.

Wannan matsayin da John Bercow shugaban majalisar dokokin kasar Britania daga Jam'iyyar Labour ya dauka dai ba zai yi wa Priministan kasar Theresa May dadi ba, musamman a kokarin da take wajen kyautata dangantaka tsakanin Amurka da Britania musamman bayan ficewar kasar daga tarayyar Turai.

Jawabin shugaban majalisar dokokin kasar ta Britania a jiya dai ya samu goyon bayan mafi yawan yan majalisar musamman yan jam'iyarsa ta Labour da kuma Scottish National Party.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky