Al'ummar Amurka Suna Ci Gaba Da Zanga -Zangar Nuna Adawa Da Bakar Siyasar Gwamnatin Trump

  • Lambar Labari†: 809642
  • Taska : Pars Today
Brief

Al'ummar Amurka suna ci gaba da gudanar da zanga- zangar nuna adawa da bakar siyasar sabuwar gwamnatin kasar ta kokarin haifar da kiyayya kan al'ummar musulmi.

Al'ummar Amurka sun gudanar da zanga-zangar ce a birane da dama na kasar a yammacin jiya Asabar, inda suka cika manyan hanyoyin jihohin Denver, Philadelphia, New York, Washington D.C da Miami da ke jihar Florida suna rera taken yin Allah wadai da bakar siyasar shugaban Amurka Donald Trump ta kokarin katange al'ummar musulmi daga shiga cikin kasar ta Amurka. 

Har ila yau masu zanga-zangar sun yi ta rera taken neman ganin gwamnatin Amurka ta janye aniyarta ta nuna kyamar bakin haure da 'yan gudun hijira daga kowace al'ummar duniya suka fito.

Tun a ranar Juma'a 27 ga watan Janairu da ya gabata ne shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan dokar takaita shigar baki 'yan kasashen waje da 'yan gudun hijira da suka fito daga wasu kasashen musulmi cikin kasar ta Amurka, kuma kasashen sune Iran, Iraki, Sudan, Somaliya, Libiya, Siriya da Yamen.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky