CIA na binciken wani Jami’in Trump akan Rasha

  • Lambar Labari†: 806715
  • Taska : RFI
Brief

Rahotanni daga Amurka na cewar Hukumar leken asirin kasar na gudanar da bincike kan wani mai bai wa shugaba Donald Trump shawara game musayar bayanan da ya yi da wasu jami’an gwamnatin Rasha.

Jaridar Wall Street Journal ta ce ana binciken ne kan Janar Micharl Flynn, daya daga cikin masu bada shawara ga shugaba Trump da aka rantsar jiya Lahadi.

Binciken ya nuna cewar Janar Flynn mai ritaya ya karbi wasu kudade inda ya halarci wani biki a Moscow, tare da zaunawa teburi guda da shugaba Vladimir Putin.

Bayanan sun ce, tsohon sojan ya yi ta waya da Jakadan Rasha a Amurka, Sergey Kislyak, kwana guda kafin Obama ya bayyana daukar mataki kan Rasha.

Sai dai kuma kakakin Trump Sean Spicer ya musanta zargin inda ya ce Flynn ya zanta ne da jekadan na Rasha a ranar Kirsimeti kuma sun yi musayar sakwannin murnar sabuwar shekara ne ta wayar hannu.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky