Wani Kwamitin Majalisar Dattawan Amurka Zai Tattauna Akan Kutsen Rasha

  • Lambar Labari†: 802954
  • Taska : VOA
Brief

Kwamitin harkokin soja na majilisar Dattijai a nan Amurka zaiyi zaman tattaunawa ta musammam a yau Alhamis domin duba matakin da gwamnatin Barrack Obama ta dauka game da tuhumar da take yiwa kasar Rasha na kutsen da tace tayi game da zaben shekarar 2016, da kuma kuntatawa wasu jamia’an diflomasiyya.

Shugaban kwamitin Sanata John McCain ya fada jiya Laraba cewa wannan kutsen da Rasha tayi tamkar tsokanar yaki ne da Amurka take yi.

A lokacinda yake zantawa da manema labarai a farfajiyar majilisa, McCain yace duk wanda yayi kokarin lalata tsarin demokaradiyyar wata kasa to kasar yake kokarin rusawa.

Yace wannan dabi’ar wata alama ce ta neman yaki.

A cikin satin da ya gabata ne dai shugaba Obama ya mayar da martini ga kasar Rasha inda ya dauki matakan takunkumin horaswa daban-daban akan hukumomin liken asiri na Rasha, wadanda Amurka ta zarga da shiga sharo ba shanu lokacin yakin neman zabe.

Haka kuma gwamnatin ta Amurka ta kori jamian diflomasiyyar Rasha har su 35.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni