Amurka Ta Dauki Matakan Horar Da Rasha Akan Shisshigin Zabe

  • Lambar Labari†: 801726
  • Taska : VOA
Brief

Shugaban Amurka, Barack Obama, ya dauki matakai da dama na horar da Rasha saboda shisshigin da tayi a cikin zaben Amurka na wannan shekara, wanda ya hada da satar bayanai ta hanyoyin duniyar gizo, da muzgunawa jami’ian diplomasiyar Amurka dake aiki a birnin Moscow, da dai sauran abubuwan da ake zargin kasar da aikatawa.

Shugaba Obama yace yana ganin matakan da ya dauka sun dace kuma sunyi daidai da abubuwan da Rasha ta aikata, wadanda Obama yace suna iya yin lahani ga muradun Amurka, sannan kuma sun taka ka’idodjin cudanyar kasashe.

Daga cikin matakan da shugaban na Amurka ya dauka harda na horad da mutane da

kungiyoyin Rasha guda 9. Haka kuma Amurka ta baiwa wasu jami’an opishin jakadancin Rasha 35 dake nan Washington sa’oi 72 su hada nasu ya nasu su bar Amurka din.

Ko bayan haka, Amurka ta haramtawa Rasha anfani da wasu manyan gidaje guda biyu na hutawa mallakar gwamnati dake jihohin New York da Maryland da MHWA ta bayyana da cewa muhimman wuraren sake jiki ne a wurin kusoshin gwamnatin ta Rasha.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky