Trump ya yi amai ya lashe

  • Lambar Labari†: 791519
  • Taska : RFI
Brief

Zababben Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya nuna cewa zai ci gaba da aiwatar da tsarin Shirin inshoran Lafiya na gwamnatin Barack Obama, bayan Sukar tsari da cewa zai Soke shi a lokacin yakin neman zaben shi.

A zantawarsa da mujallar Wall Street Journal, ranar ta biyu a c igaba da aiwatar da sauye-sauye karban mulki, Trump ya ce zai iya ci gaba da aiwatar da wasu muhimman abubuwa da ke kunshe a shirin inshorar lafiyar.

A baya dai Trump ya bayyana shirin tamkar masifa ga kasar Amurka.

Tun bayan nasara Mista Trump da ta zo wa duniya da bazata, zabebben shugaban kasar yake ta sanar da sauye-sauye kan alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zabensa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky