Hukumar FBI Ta Wanke Hillary Clinton

  • Lambar Labari†: 790421
  • Taska : VOA
Brief

Jiya Lahadi shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta FBI James Comey ya shaidawa majalisar wakilan Amurka cewar rahotonsa akan Hillary Clinton 'yar takarar jam'iyyar Democrat da ya bayar watan Yulin shekarar nan bai canza ba, wato bata aikata wani laifi ba da za'a iya tuhumarta a kai.

James Comey ya bada sanarwar ce cikin wata wasika da ya aikawa majalisar wakilai bayan hukumar ta kammala binciken wasu karin wasikun email da aka gano makon jiya.

Hukumar ta bude maganar ce biyo bayan binciken da ta yiwa tsohon dan majalisa Anthony Weiner wanda matarsa da suka rabu da ita ta hannun daman Hillary Clinton ce. A wannan binciken ne hukumar tayi kicibis da wasu wasikun email da suka fito daga Hillary Clinton.

Cikin wasikarsa James Comey yace ma'aikatan hukumar sun yi aiki tukuru dare da rana suna binciken wasikun. Bisa ga tasu fahimtar basu ga wani sabon abu ba da zai sa su canza matsayinsu akan tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar kuma 'yar takarar shugaban kasa Hillary Clinton.

A rahotonsa na watan Yuli yace ko shakka babu Hillary Clinton tayi sakaci akan yadda ta kula da labarai amma babu niyyar aikata wani laifin da za'a tuhumeta dashi.

Jennifer Palmieri tace sun yi farin ciki cewa an kawo karshen wannan badakalar. Tace tun farko sun fada babu wani abu sabo da hukumar FBI zata kara ganowa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky