Za a yi maguɗi a zaɓen Amurka — Trump

  • Lambar Labari†: 769593
  • Taska : BBC.COM
Brief

Dan takarar shugaban Amurka a karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump ya ce mai yiwuwa za a yi magudi a zaben kasar da za a yi a watan Nuwamba.

Mista Trump ya shaida wa wani taron yakin neman zabe a birnin Columbus na jihar Ohio cewa yana ta jin labarin cewa ba za a yi zaben gaskiya ba.

Sai dai bai bayar da wata hujja a kan zargin da ya yi ba.

Donald Trump ya bayyana abokiyar hamayyarsa ta Democrats Hillary Clinton da cewa "ita shaidaniya ce", a yayin da yake ci gaba da shan suka daga 'yan jam'iyyars

Mista Trump ya zargi Sanata Bernie Sanders da marawa Misis Clinton baya.

Ya kara da cewa Mista Sanders ya yi yarjejeniya da shaidan, domin kuwa Hillary shaidaniya ce.

Dukkan jam'iyyun Democrats da Republican dai -- ciki har da tsohon dan tankarar Republican din John McCain -- sun yi Allah wadai da kalaman da Mista Trump ya yi amfani da su kan iyayen wani sojan Amurka musulmi, Humayan Khan da aka kashe a kasar Iraqi.

Trump dai ya yi wa mahaifiyar Humayan shagube bayan mahafinsa ya caccake shi kan jahincinsa game da addinin Musulinci.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky