Kungiyar ISESCO Ta Mika Sakon Ta'aziyyar Rasuwar Muhammad Ali

  • Lambar Labari†: 758363
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Hukumar kula da ayyukan ilimi da al'adu ta kasashen musulmi ISESCO ta isar da sakon ta'aziyyar rasuwar zakaran wasan dambe na duniya marigayi Muhammad Ali.

A cikin wani bayani da babban daraktan hukumar Usman Tuwaijari ya fitar a jiya, ya bayyana Muhammad Ali a matsayin wani mutum musulmi abin koyi ga kowa, domin ya kasance mutum mai kyawawan dabiu da tausayi da kuma taimako ga marassa galihu, kamar yadda ya kasance mai kare hakkokin raunana.

Ya ce Muhammad Ali ya yi amfani da dimbin dukiyarsa wajen gudanar da ayyukan alkhairi da gina cibiyoyin taimaka ma marassa galihu da marayu a cikin Amurka da kasashen duniya daban-daban, da kuma taimaka ma cibiyoyin da makarantu na addinin muslunci, kamar yadda kuma ya kasance a sahun gaba wajen yaki da nuna wariyar launin fata da zaluncin da aka yi wa bakaken fata a kasar Amurka.

A ranar Juma'a da ta gabata 3 ga watan Yuni 2016 Muhammad Ali ya rasu yana da shekaru 74 a duniya, bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky