Dan Bindiga Ya Nemi Shiga Fadar Shugaban Amurka

  • Lambar Labari†: 755473
  • Taska : RFI
Brief

Jami'an tsaron fadar Shugaban kasar Amurka White House na chan suna binciken musabbabin da ya kai wani mutun kusa da fadar Shugaban kasar har ya yi harbi da bindiga jiya Juma'a.

Bayanai na nuna Shugaban Amurkan Barack Obama baya kusa da fadar a lokacin da aka kwashe awa daya ana cikin wani hali a harabar fadar Shugaban kasar, amma daga bisani an shaida masa abinda ya faru.

Robert Hoback, kakakin fadar ya bayyana cewa mutumin tunkarar fadar yayi da bindiga yana harbi, amma kuma jami'an tsaron fadar sunyi ta maza, bayan da suka yi ta daka masa tsawa mutumin ya ki ji, nan take wani Jami'in tsaro ya bindige mutumin amma bai mutu ba nan take, an kwashe shi zuwa asibiti.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky