'Yan sanda sun tsare tsohon shugaban Brazil

  • Lambar Labari†: 738764
  • Taska : bbc
Brief

'Yan sanda a kasar Brazil sun tsare tsohon shugaban kasar, Luiz Inacio Lula da Silva, a ci gaba da binciken da suke yi kan cin hanci da rashawa.

An kai samame a wurare da dama da ke da alaka da shi, ciki har da gidansa da kuma wata cibiya mai suna Lula Institute.

Ana yin binciken ne kan babban kamfanin mai na kasar, wato Petrobras.

Ana sa ran za a yi wa Lula tambayoyi a kan zargin da ake cewa yana da hannu a karbar hanci a wasu kasuwanci da kamfanin ya gudanar.

Cibiyar ta Lula Institute ta ce tsohon shugaban ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa.

Lula da Silva ya zama shugaban kasar Brazil daga shekarar 2003 zuwa 2011.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky