Amurka ta bukaci Rasha da Turkiyya su dinke barakar da ta shiga tsakaninsu

  • Lambar Labari†: 722510
  • Taska : RFI
Brief

Shugaban Kasar Amurka Baracak Obama ya roki kasashen Rasha da Turkiyya da su dinke barakar da ke tsakanin su dan mayar da hankali kan yaki da mayakan ISIS.Obama ya ce ISIS ce babbar makiyar su maimakon cacar bakin da suke kan kakkabo jirgin Rasha

Bayan wata ganawa da shugaba Barack Obama ya yi da Recep Tayyip Erdogan, shugaban ya bayyana karara cewar, Turkiyya kasa ce dake cikin kungiyar kawancen tsaron NATO kuma Amurka na goyan bayan kare kan ta da kuma sararin samaniyar ta.

Obama ya ce kowa ya fahimci cewar suna da makiya guda, wanda itace kungiyar ISIS, saboda haka yana da kyau su mayar da hankali akan ta.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Erdogan ya bayyana cewar shima a shirye yake su sasanta da Rasha dan fuskantar gaba.

Shi kuwa Sakataren kungiyar kawancen tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya ce abinda ke gaban su shine kwantar da hankalin kasashen biyu da kuma kaucewa sake aukuwar matsalar da aka samu.

A baya Firaministan Turkiyya Ahmet Davutoglu ya ce ba zasu nemi gafarar kasar Rasha ba.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky