Amurka:Ta Ce Za Ta Goyi Bayan Turkiya A Matsayinta Na Manba A Kungiyar Nato

  • Lambar Labari†: 721546
  • Taska : HAUSA.IR
Brief

Amurka ta ce za ta goyi bayan gwamnatin Turkiya a matsayin ta na manba a kungiyar NATO

Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai dangane da firicin magabatan Turikiya na cewa sun kakkabo jirgin Rashan ne saboda ya take hurumin sararin samaniyar kasar, mista Mark Turner mai magana da yawun ma’aikatar harakokin wajen Amurka ya ce a yanzu ba su yanke hukunci cikin gaggawa ba, amma ko yaya ta ke ciki za su tsaya a bayan gwamnatin Turkiya a matsayinta na aminiyarsu kuma manba a kungiyar Nato.

 Mista Turnar ya ce hakin kasar Turkiya ne da ta kare hurumin sararin samaniyar kasar ta.

A bangare guda babban saktaren kungiyar Nato ya bayyana cewa zai kira taron gaggawa kamar yadda Turkiya ta bukata a tattauna wannan matsala.


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky