AN GANA TSAKANIN SARKIN SAUDI AREBIYA DA SARKI SALMAN DA SHUGABAN AMURKA BARACK OBAMA

  • Lambar Labari†: 709397
  • Taska : Almayadeen
Brief

A yau ne aka gana da shugaban kasar Saudi Salman bin Abdulaziz da kuma shugaban kasar Amurka Barack Obama a wata ziyara da y akai kasar AMruka ind asuka tattauna game da batun fadada yaki da suka ce suna yi da ta'adanci ,
har ila yau sun tattauna game da batun halin da ake ciki a kasar SIriya da Yaman , da kuma batun yarjejeniyar da aka cimma kan shirin nukiliyar kasar Iran,
to sai dai wanna ganawa tana zuwa ne a daidai lokacin da kasar sausiya da kawayenta suke ci gaba da kai hare-haren ta'adancin kan fararen hula a kasar Yaman.

 Shugaban kasar Amurka da sarkin saudi Arebiya sun gana a birnin Washington na Amurka kan yakin kasar Yaman da Siriya.

 

Rahotanni sun bayyana cewa sarkin kasar Saudi Arebiya Salaman bin Abdulaziz ya kai ziyara kasar Amurka ne a yau , inda ya gana da shugaban kasar Barack Obama kuma sun tatauanwa game da batun hanyoyin da za su bi wajen fadada fada da sukace suna yi da ta’dancin da kuma halin da ake ciki a kasashen Siriya da Yaman, da kuma yarjejeniya da aka cimma kan shirin nukiliyar kasar Iran.

 

A nashi bangaren shugaban kasar Amurka a lokacin taron manema labaran na hadin guiwa da suka gudanar Obama ya nuna cewa yana tare da kasar saudiya wajen nuna damuwa game da halin da ake ciki a kasar Yaman, kuma za su ci gana da kasancewa domin ci gaba da yaki da ta’adanci da suka yi

,

Daga karshe sarkin na saudiya Salman bin Abdulaziz ya jaddada game da muhimmancin kara samun dagantaka tsakaninsu da kasar Amurka a bangarori daban-daban, musamman ma wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, sai dai wannan ziyara tana zuwa ne adaidai lokacin da dakarun hadin guiwa karkashin jagorancin kasar saudiya suke ci gaba da kai hare-haren kan fararen hula a kasar Yaman.288

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky