AN GUDANAR ZANGA-ZANGAR KIN JININ ZIYARAR NATANYAHO PIRA MINISTAN ISRA'ILA A BIRTANIYA

  • Lambar Labari†: 709100
  • Taska : alalam
Brief

Dubun dubatan alummar Birtaniya ne suka gudanar gagarumar zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da ziyarar da pira ministan Isra'ila Binyanmin Natanhu zai kai Birtaniya inda suka neman gwamnatin kasar da ta soke ziyarar tasa, tare da bayyana shi matsayin wanda ya tafka laifukan yaki, lamarin da gwamnatin tayi wasti da shi kuma ta nuna cewa bisa dokokin kasar duk wanda ya kawo mata ziyara to yana karkashin kulawarsu kuma za su bari a kama shi ba.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

An gudanar da gagarumin gangami a birnin London na birtaniya domin nuna kin ji nin Ziyarar da Pira ministan Isra’ila Binyamin Natanyaho zai kai kasar .

Kimanin Mutanen Birtaniya dubu casa’in ne suka yi wani gangami na neman gwamnati kasar da ta soke ziyarar da aka shirya pira ministan Israi’la Binyamin Natanyaho zai kai kasar a ranar 9 ga watan Satumbar da muke ciki, saboda kasancewarsa wanda ya tafka laifukan yaki. Sai dai mahukumatan kasar sun yi kunnen uwar shegu da su da hujjar cewa bisa dokokin kasar wanda aka gayyata to yana karkashin kariyarta don haka ba za ta bari a kamashi ba,

A nata bangaren mai kula da hulda da jama’a a kungiyar kare hakkin palasdinawa Zahra Birawi ta bayyana cewa matsayin gwamnatin kasar kan wannan batu ya yi hannun riga da ra’ayin Alummar kasar na kare hakokin palasdinu kuma ya yi karo da rajin tabbatar da Adalci da gwamnatin kasar ke shelantawa tana yi, kuma hakan zai kawo cikas game da batun tabbtar da Adalci ga Alummar Palasdinu da suke dandana kuda a hannun gwamnatin mamaya ta Isra’ila.

 

 

 

 

 

 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky