Amurka ta gargadi Amurkawa a Kenya

  • Lambar Labari†: 700907
  • Taska : RFI
Brief

Amurka ta gargadi ‘yan asalin kasarta da ke zaune a Kenya kan yiwuwar harin ta’addanci da za iya fuskanta gabanin ziyarar da Shugaba Obama zai kai a Kasar

Obama zai kai ziyara a kasar Kenya, Inda zai gabatar da jawabi a taron zuba hannayen jari na kasashen duniya da za bude a ranar 24 ga wannan watan na Yuli.

lura da girman taron, Amurka tace ‘yan ta’adda za su iya samun damar kaddamar da hare hare ga mahalarta lamarin da ya sa ta bukaci Amurkawa su yi taka-tsantsan matuka kan sha’anin tsaro.

Kasar Kenya ta fuskanci hare haren ta’addanci daga kungiyar Al-Shebab ta Somaliya, inda a watan Afrilun aka hallaka mutane 148 a wani hari da mayakan Shabab suka kai a jami’ar Garissa ta Kenya kuma dalibai ne akasarin wadanda harin ya ritsa da su.

Kazalika a shekarar 2013, mayakan Al-shebab sun harbe har lahira mutane 67 a katafaren shagon Westgate da ke birnin Nairobi.

A watan mayun daya gabata, Ofishin jakadancin Amurka a birnin Nairobi ya yi irin wannan gargadin ga Amurkawa akan su kula matuka dangane barazanar hare haren ta’addanci da ya hada da tashe tashen hankula a wasu sassa na kasar Kenya.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky