Obama zai halarci jana'izar bakaken fata a Amurka

  • Lambar Labari†: 696925
  • Taska : rfi
Brief

Shugaban Amurka Barack Obama a ranar juma’a mai zuwa zai ziyarci garin Charleston na jihar Carolina, inda wani dan bindiga farar fata mai suna Dylaan Roof ya kai hari tare da kashe bakaken fata 9 a wata mujami’a.

Obama da mataimakinsa Joe Biden za su halarci jana’izar shugaban wannan coci mai suna Clementa Pinckney tare da gabatar da gajeran jawabi a wurin.

Shi kuwa gwmanan jihar Carolina ta kudu inda lamarin ya faru, Nikki Haley, ya bukaci a sauke tutar nan da aka rika amfani da ita a lokacin yakin basasar Amurka kimanin shekaru 150 da suka gabata, wadda ake kallo a matsayin tutar nuna wariyar jinsi tsakanin bakake da farare na kasar, amma yanzu haka take kan ginin Majalisun dokokin kasar.

Tuni dai jami’an tsaro suka kama Dylaan Roof mai shekaru 21 a duniya yayin da aka gurfanar da shi a gaban kotu, in da tuhume shi da aikata laifin kisan kai.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky