An gurfanar da dan bindigar Charleston

  • Lambar Labari†: 696328
  • Taska : bbc
Brief

Wani abokin dan bindigar nan da ya harbe Amurkawa 'yan asalin Afrika a wani coci ya ce daama dan bindigar da ake tuhuma ya yi batun cewa yana son ya kashe wasu dalibai a wata Jami'a dake kusa da su.

Christon Scriven yace Dylann Roof din ya taba batun cewar zai kai hari a Jami'ar Charleston - to amma ya yi shiru a lokacinda aka yi masa tambayoyi.

A gurfanarsa ta farko gaban Kotu, 'yan uwan mutanen da aka kashe sun gaya ma Roof din dan shekaru 21 da haihuwa cikin halin da suka shiga, to amma wasunsu sun ce, sun gafarta masa.

Shugaba Obama ya yaba ma irin yadda mutane suka hada kai suna juyayin abinda ya faru, yana mai cewar dole ne a sake nazarin dokoki na mallakar bindiga.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky