IS: Amurka ta ware tukwicin dala miliyan 20

  • Lambar Labari†: 688571
  • Taska : bbc
Brief

Amurka ta yi tayin bayar da ladar dala miliyan 20 a matsayin tukwici ga wadanda suka bayar da bayanai game da wasu shugabannin kungiyar IS 4.

Mutanen sune Abdulrahman Mustapha Al-Qaduli, da Abu Mohammed Al-Adnani, da Tarkhan Tayumurazovich Batirashvili da kuma Tariq Bin Al-Tahir Bin Falih Al-Awni Al-Harzi.

Al-Adnani shi ne kakakin kungiyar ta IS, yayin da Batirashvili kuwa, kwamandan yaki ne na kungiyar a arewacin Syria, shi kuwa Tariq Al-Harzi shi ne mai kula da masu kunar bakin wake na kungiyar.

A baya dama Amurkan ta yi tayin bada ladar dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayani a kan mutumin daya ayyana kansa a matsayin shugaban kungiyar IS, Abubakar Al-Baghdadi

Kungiyar IS ta ce ita keda alhakin kai hari a birnin Dallas na jihar Texas inda ake gasar nuna bajintar zanen barkwanci da aka kwaikwayi Annabi Muhammad (S.A.A.W).ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky