Ana gasar zanen barkwancin Annabi{S.A.A.W} a Texas

  • Lambar Labari†: 688186
  • Taska : bbc
Brief

'Yan sanda a jihar Texas ta Amurka sun harbe wasu mutane biyu har lahira, wadanda suka bude wuta kan jami'in tsaro a wani wuri da ake gudanar da gasar nuna bajintar zanen-zanen barkwancin da aka kwaikwayi Annabi Muhammad (S.A.A.W).

Kungiyar American Freedom Defence Initiative, wadda ta shirya gasar, ta tanadi dala dubu 10 a matsayin babbar kyauta ga wanda zanen sa ya fi kwaikwayon Annabi Muhammad{S.A.A.W}.

Mista Geert Wilders, dan kasar Holland da aka sani da kin jinin musulunci, shi ne babban mai jawabi a wajen gasar.

Jama'a a yankin kuma sun rufe sana'o'in su saboda harbe harbe.

Nuna hoto ko zanen batanci game da Annabi Muhammad (S.A.AW) abu ne da yake bata ran Musulmai a wurare daban-daban.

A shekarar 2006 an ta gudanar da zanga zanga lokacin da wata jaridar kasar Denmark ta buga wani zanen barkwanci da ta nuna cewa Annabi Muhammad{S.A.A.W} ne.

A watan Janairun wannan shekara ma, kimanin mutane 12 ne wasu 'yan bindiga suka kashe a kamfanin wata mujalla a Faransa wadda ta buga irin wannan zane na barkwanci.ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky