dokar hana fita a Baltimore na Amurka

  • Lambar Labari†: 686912
  • Taska : bbc abna
Brief

An sanya dokar ta-baci da kuma dokar hana fita ta tsawon mako guda a birnin Baltimore na kasar Amurka domin kwantar da tarzomar da jama'a suke yi.

Wasu jami'an gwamnati sun ce tarzomar da ake yi ita ce mafi muni tun bayan wadda ta biyo bayan kisan Martin Luther King a shekarar 1968.

Magajiyar garin birnin Baltimore, Stephanie Rawlings Blake, ta yi Allah wadai da abin da ta bayyana sace-sace da barnata kayayyaki da kuma kona gidaje da ake yi da sunan tarzoma.

Tarzomar ta taso ne bayan amutuwar Freddie Gray, wani Ba'Amurke bakin fata mai shekaru 25 da 'yan sanda suka yi wa mummunan rauni lokacin da suke tsare da shi.

Jami'an 'yan sanda sun ce masu zanga-zangar sun jejjefe su da duwatsu, da bulo da kuma kwalabe, lamarin da ya sa 'yan sanda 15 suka samu ranuka.ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky