Obama ya soki Firaminista Netanyahu

  • Lambar Labari†: 678355
  • Taska : bbc
Brief

Shugaba Obama ya zargi Firaministan HK Isra'ila Benjamin Netanyahu da sa a dauka cewa abu ne da ba zai taba yuwuwa ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Palasdinawa.

Wannan shi ne kalaminsa na bainar jama'a na farko tun bayan da  Netanyahu, ya yi nasara a zaben da aka yi ranar Talatar da ta gabata.

Shugaba Obama, ya ce Amurka, ta cigaba da yin amanna cewa, samar da kasashe biyu na HK Isra'ila da Palasdinu, ita ce hanya daya tilo ta tabbatar da tsaro da zaman lafiyar HK Isra'ila.

Mr Obama ya soki, kalaman ranar zabe na Netanyahu, inda Firaministan ya yi gargadin cewa tururuwar da Larabawa ke yi zuwa kada kuri'a, suna yi ne domin adawa da muradin HK Isra'ila.ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky