Ba da musulunci muke yaki ba — Obama

  • Lambar Labari†: 671969
  • Taska : bbc
Brief

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce duniya na yin yaki da 'yan ta'adda ne wadanda suka fandarewa Musulunci, ba da addinin musuluncin ba.

Mr Obama ya bayyana haka ne a wani taro kan yaki da ta'addanci na kwanaki uku a birnin Washington,.

Ana yin taron ne domin nemo hanyoyin da za a dakile ayyukan masu tayar da kayar baya a duniya.

Shugaba Obama ya ce dole ne duniya ta tashi tsaye ta tunkari munanan akidoji wadanda kungiyoyi irin su IS ke amfani da su wajen tsokano tashin hankali da kuma cusawa matasa mummunar akida.

Ya kara da cewa lallai ne a dauki matakan kawar da matsalolin da ke sanya wa matasa suna shiga cikin kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi.

Wakilai daga kasashe fiye da sittin ne suka halarci wannan taro, hakan kuma ya biyo bayan hare-haren da aka kai kasashen Denmark da Faransa da kuma Australia.ABNA


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky