Za’a sabunta zanga-zangar kyamar gwamnati a Amurka

  • Lambar Labari†: 657974
  • Taska : RFI HAUSA
Brief

A kasar Amurka wani lokaci a yau ne aka shirya gudanar da wata gagarumar zanga-zangar kara nunawa hukumomin kasar fa, ba’a aminta da yadda ‘yansanda fararen fata ke kisan gilla ga fararan Hula bakaken fata ba

An ce dai a wannan karon zanga-zangar za ta game biranen kasar da dama, kuma masu zanga-zangar na kokarin matsawa kasar Amurka lamba ne akan bukatar a dauki mataki ga yadda a baya-bayan nan ma’aikata suka kama nunawa bakaken Fatar kasar banbanci.

Idan ana iya tunawa a farkon watan jiya ne aka bada labarin kisan da wani dansanda farar fata ya yiwa wani farar Hula bakar fata, amma hukumomin kasar ta amurka basu yi komai akai ba.

Kasar Amurka dai na kan gaba ga gangamin kare ‘yancin bil’adama a Duniya, amma wannan al’amarin ya haifar da dari-darin da ake akan sahihancin adalcin da kasar Amurka ke cewar tana kwatantawa a tsakanin al’ummar kasar.ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky