Biritaniya za ta ninka yawan sojojinta a Nigeria

  • Lambar Labari†: 726184
  • Taska : BBC
Brief

Sakataren tsaron Biritaniya ya ce kasarsa za ta ninka yawan sojojinta da ke Najeriya domin taimakawa wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Micheal Fallon ya bayyana haka ne bayan ganawar sirrin da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.

A shekara mai zuwa ne ake sa ran Biritaniya za ta kara adadin dakarunta zuwa 300 a Najeriya domin ganin an murkushe mayakan Boko Haram.

Dakaru na musamman ne wadanda suka kware wajen dakile hare-haren abubuwa masu fashewa da kuma bayar da shawarwari ta fannin kiwon lafiya.

Kazalika, akwai wasu sojojin wadanda za su taimaki rundunar sojin sama na Najeriya a kan yadda ake murkushe ta'addanci.

A wannan shekarar dai akwai sojojin Biritaniya 150 da ke taimakawa ta fannoni daban-daban na Najeriya.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky