-
Iran: An Rataye Manyan Mambobin Mafia Na Fashi Da Makami A Yau
Wannan ƙungiya, a cikin shekaru da yawa, a Tehran da garuruwa ciki har da Karaj, Qom, Mashhad, Kuhdasht, da yankuna na Mazandaran da Isfahan, ta aikata fashi da makami da kuma haifar da tsoro da firgita a tsakanin al’umma.
-
Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Da Matsayin Ilimi Da Aiki Na Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene'i
Sanin Ilimin Fiqihu da ƙwarewa a tushen fiqhu da darussan makarantar addini, kafa cibiyoyin ilimi, ƙwarewa a ilimomin zamani da sabbin fasahohi, tsara manyan shirye-shiryen dabaru a fannonin soji da jihadi, tare da gudanar da ayyuka na asali a batutuwa daban-daban na al'adu da zamantakewa, a lokaci guda tare da ƙirƙirar hanyoyin sadarwa na cibiyoyin tallafi, wasu sassa ne da ba a bayyana ba na rayuwa da yanayin ilimi da aiki na Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene'i.
-
Sojojin Najeriya Da Africom Na Ci Gab Da Gudanar Da Atisayen Hadin Gwiwa A Bauchi
Najeriya: Shugaban Kasa Ya Ba Da Umarnin Aiki Don Ceto Wadanda Aka Sace
Shugaban Najeriya ya umarci sojoji da hukumomin tsaro su ƙaddamar da wani aiki na gaggawa don ceto wadanda aka sace a jihar Nijar, a daidai lokacin da rundunar sojin Amurka a Afirka ta bayyana cikakken bayani game da atisayen soji na hadin gwiwa a Bauchi
-
Iran Ta Yi Gargadi Ga Ƙungiyoyin Takfiriyya; Kada Ku Kusanci Iyakokin Iran
Kwamandan sojojin ƙasa ya yi gargadi ga ƙungiyoyin takfiri da abokan gaba da ke zaune a ɗaya gefen iyakokin: Iyakokin Iran jan layi ne, kuma duk wani motsi, mugun aiki, ko mataki a kansu, zai fuskanci martani mai ƙarfi mai murkusarwa.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Yadda Isra’ila Ta Kai Hari A Al-Zawayda Gaza
Gobara mai yawa da ginshiƙan hayaki, bayan harin sama na Isra'ila a kan gidaje da dama da tantunan mazauna 'yan gudun hijira a Al-Zawayda na Gaza, sun ɗauki hoton ci gaba da tashin hankali a tsakiyar tsagaita wuta mai rauni a wannan yanki.
-
Janar Na Lebanon: Iran Ba Za Ta Taɓa Daina Tallafawa Hizbullah Ba
Wani masanin harkokin soji da dabaru na Lebanon ya ce, Iran har yanzu tana da manyan katunan nasara a yankin, kuma ba za ta taɓa daina tallafawa Hizbullah ba.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Bikin Maulidin Annabi (S.A.W) A Gujranwala, Pakistan
A daidai lokacin da ake cikin kwanakin Maulidin Annabi (S.A.W) mai albarka, malamai da daliban jami'ar Al-Mustafa (S.A.W) a birnin Gujranwala na Pakistan, ta hanyar gudanar da muzahara mai girma na Maulidin Annabi (S.A.W), sun nuna ƙauna da soyayya mai zurfi ga Annabi Maɗaukaki (S.A.W).
-
Saudiyya Ta Sanya Sabbin Dokoki Masu Tsanani Ga Ma'aikata Baƙi
Saudiyya ta sanya sabbin dokoki masu tsanani ga ma'aikata baƙi, waɗanda suka haɗa da tarar kuɗi har zuwa ɗauri.
-
Iran: Kwamandan Sojojin Pakistan Ya Isar Da Sharuɗɗanmu Ga Washington
Wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na "Tasnim" cewa, kwamandan sojojin Pakistan bai zo da sakonnin barazana ga Iran ba, kuma ta tabbatar da cewa, ya yi aiki a matsayin mai sasanci don isar da sharuɗɗan Tehran game da mashigar Hurmuz zuwa Washington, mafi muhimmanci shine bin yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad.
-
Sayyid Houthi: Za Mu Ci Gaba Da Ma'aunin "Killacewa A Kan Killacewa"
Yamen: Miliyoyin Mutane Sun Yi Murnar Maulidin Annabi A Sana'a
Shugaban ƙungiyar Ansar Allah, a cikin jawabinsa na Maulidin Annabi, ya jaddada danfarewarsu ga hadin kan fagage don kawar da shirin "Babbar Isra'ila," yana mai jaddada ɗora wa Saudiyya alhakin killacewa da tashin hankali, da kuma tabbatar da daidaiton kai hari a kan taron sojinta.
-
Matsayin Yemen A Kan Zaluncin Amurka Da Yahudawa Ya Tabbata Ce Ne Maras Canzuwa
Yamen: Saudiyya Ta Dauki Shekaru 12 Ta Na Aiwatar Da Ta’addanci A Yamen
Sayyid Abdul-Malik Badrid-Din Houthi, babban shugaban Ansarallah na Yemen, a cikin jawabinsa na bikin Maulidin Annabi (S.A.W) a Sana'a, yana mai jaddada hakkin al'ummar Yemen na kawo ƙarshen killacewar zalunci na shekaru 12 da gwamnatin Saudiyya ta yi, ya ce: Gwamnatin Saudiyya, wadda ta hana al'ummar Yemen dukiyar ƙasarsu, kuma ta rufe filayen jiragen sama, ita ce ke da cikakken alhakin dukkan sakamakon hakan, kuma muna tare da al'ummar Iran da tsarin Musulunci.
-
Me Ya Sa Turkiyya Ba Ta Mayar Da Martani Ga Hare-haren Isra'ila A Siriya Ba?
Harin baya-bayan nan na gwamnatin yahudawa a kan filin jirgin sama na soji na Abu Al-Zuhur a gabashin Idlib, ya sake tayar da yiwuwar arangama kai tsaye tsakanin Turkiyya da Isra'ila a ƙasar Siriya; duk da haka, da alama Ankara da Damascus a yanayin da ake ciki yanzu sun fi son yin haƙuri da dogaro ga goyon bayan Amurka, su guji shiga rikici kai tsaye da Tel Aviv.
-
Amir Hatami: Za Mu Yaƙi Har Zuwa Ƙarni 20 Kuma Ba Za Mu Bari A Cutar Da Iran Ba
Iran: Hanya Ɗaya Tilo, Da Harshen Ƙarfi, Mu Fahimtar Da Makiya Cewa Ba Za Su Iya Yin Abin Da Suke So Ba.
Kwamandan sojoji ya ce: Dole ne mu hana makiya cimma burinsu, kuma mu dandana musu ɗacin rashin nasara har su gane cewa, Iran ba wurin da za a zo daga ƙarshen duniya ba, a ce za a canza taswirar ƙasarta ba ce. Za mu yaƙi har zuwa ƙarni 10, ƙarni 20, kuma ba shakka ba za mu bari hakan ta faru ba; hanya ɗaya tilo ita ce, da harshen ƙarfi, mu fahimtar da makiya cewa ba za su iya yin abin da suke so ba.
-
Isra’ila Na Ci Gaba Da Lugudan Wuta A Kudancin Lebanon
Bisa ga alkaluman hukuma na Lebanon, hare-haren Isra'ila, waɗanda suka ci gaba tun daga 2 ga Maris da ya gabata, har yanzu sun haifar da shahadar mutane 4,348, da raunata 12,307. Haka kuma, fiye da 'yan ƙasar Lebanon miliyan ɗaya sun rasa gidajensu daga garuruwa da ƙauyuka.
-
A Bikin Karrama Iyalan Shahidai Na Gwamnati;
Dr. Pezeshkian: Mutane Masu Dawainiya Da Sadaukarwa Na Iran Ne Aka Shahadantar
Shugaban kasar Iran, yana mai jaddada cewa, a kan hanyar biyan buƙatun kowane ɗayan al'umma, muna aiki fiye da ra'ayoyin bangaranci, siyasa, da jam'iyya, ya bayyana cewa: Tsarawa da aiwatarwa don hidimar al'umma a cikin al'umma, dole ne su dogara ga shaidar ilimi. Ɗaya daga cikin ayyukan makiya a kan tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, shine kisan kai da shahadantar da mutane masu tasiri da ƙwararru a cikin shekaru da yawa.
-
Shekh Zakzaky {H}: Duk Karatun Da Zai Amfane Ka Duniya Da Lahira, Ya Kuma Amfanar Da Al’umma, Ibada Ne.
Da safiyar ranar Asabar, 22 ga Agusta 2026, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya rufe taron ɗaliban Firamari da Sakandire na IVC a Abuja, wanda Dandalin Ɗaliban Harkar Musulunci ke shiryawa a duk lokacin hutun yara.
-
Ka Ga Inda Ake Mauludi:
Yemen: Al-Hudaydah Na Shirye-shiryen Karbar Bakuncin Miliyoyin Mutane A Bikin Maulidin Annabi (S.A.W)
A daidai lokacin da ranar haihuwar Annabi (S.A.W) ke gabatowa, jami'an lardin Al-Hudaydah na Yemen sun sanar da kammala shirye-shiryen aiwatarwa, ayyuka, lafiya, tsaro, da kafofin yada labarai, don gudanar da babban bikin wannan lokaci; bikin da za a gudanar gobe tare da halartar jama'a da yawa a wurare uku.
-
China Ta Ja Kunnen Amurka A Kan Takunkuman Iran; Beijing Ta Jaddada Kare Muradunta
Ma'aikatar harkokin wajen China, tare da yin gargadi game da sabbin takunkumin Amurka a kan Iran, ta jaddada cewa, Beijing tana bin abubuwan da ke faruwa game da waɗannan matakai a hankali, kuma idan ya cancanta, za ta ɗauki matakan da suka dace don kare haƙƙoƙinta da muradunta.
-
Hashdush Sha'abi: Gwagwarmayar Iraki Tsuro Daga Zuciyar Al'ummar Shi'a Domin Yaƙi Da Mamaya
Hashdush Sha'abi: Ba Za Mu Aiwatar Da Abin Da Washington Ke Bukata Ba
Shugaban yaɗa labarai na Hashdush Sha'abi, a wani ɓangare na maganganunsa, yana mai ƙin duk wani biyayya ga Amurka, ya ce: Mu ba jiha ko wani sashe na Amurka ba ne, kuma ba za mu aiwatar da abin da Amurka ke nema ba.
-
Libiya: Kama Karyar Siyasa Da Karancin Jari; Cikas Biyu Manya Na Hana Bunkasar Masana'antar Man Fetur Ta Libiya
Shugaban kamfanin man fetur na ƙasa na Libiya ya sanar da cewa, wannan ƙasa, don farfado da matsayinta a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu samar da man fetur a duniya, da kuma haɓaka albarkatun man fetur da iskar gas, tana buƙatar kimanin dala biliyan 40 na zuba jari, kuma duk da mallakar mafi girman albarkatun man fetur da aka tabbatar a Afirka, rashin kwanciyar hankalin siyasa, karancin jari, da rashin tsaro, sun hana amfani da fiye da rijiyoyin man fetur 60 da aka gano, da kuma ƙara samarwa zuwa ganga miliyan biyu a kowace rana.
-
Mutane Uku Ne Su Kai Shahada Ciki Harda Wani Karamin Yaro A Nablus Da Gaza
Wani yaro ɗan Falasdinu a sansanin Askar da ke gabashin Nablus, yayi shahada sakamakon harbin sojojin gwamnatin yahudawa, kuma a hare-hare daban-daban da aka kai a sansanin Al-Nuseirat da garin Al-Zawayda a tsakiyar zirin Gaza, Falasdinawa biyu sun yishahada kuma wasu bakwai sun jikkata.
-
Atwan: Zaɓin Sojin Trump A Kan Iran Ya Sha Kaye | Takunkumin Tattalin Arziki Ma Zai Sha Kaye
Abdul Bari Atwan, babban manazarcin harkokin dabaru na yankin, a cikin wata makala, yana mai nuni ga sabuwar dabarar Donald Trump na killacewa da takunkumin tattalin arziki a kan Iran, ya rubuta cewa, komawa ga wannan dabara yana nufin rashin nasarar zaɓin soji wajen cimma burin wannan yaƙi, kuma ya jaddada cewa, takunkumin tattalin arziki, kamar zaɓin soji ne, shi ma zai sha kaye, domin Iran ƙasa ce mai girma kamar nahiya, tana da yawan jama'a sama da miliyan 95, kuma ƙasarta mai albarka ce, ba za ta taɓa jin yunwa ba.
-
Sheikh Yaqoub: Manzon Allah Ya Cancanci Mu Yi Murna Da Haihuwar Shi: Ko Ba Lada Mun Taya Allah Aiki.
Duk abin da za mu yi saboda Manzon Allah (SAWW), to ba mu yi komai ba. Ko da ma ba za a ba mu lada ba, Manzon Allah (SAWW) ya cancanci mu yi murna da samuwarsa, domin Allah (SWT) yana son Manzon sa, mu ma muna son sa. Saboda haka, gashi nan, muna yi, ko ba a ba mu lada ba, mun taya Allah aiki. Kuma wallahi, da Allah (SWT) bai son wannan abin (Maulud) da muke yi, da tuni an bari… da tuni an bar shi. Domin Allah yana kishin Manzon sa sosai.
-
Mossad Ta Yi Rashin Nasarar Da Ba A Zata Ba A Ayyukan Leken Asiri A Kan Iran
Shafin yanar gizo na The Intercept, a cikin wani rahoto, yana mai nuni ga "rashin nasara ta tarihi na Mossad" a cikin ruɗani game da canjin mulki a Iran, ya rubuta cewa, rashin nasarar wannan hukumar leken asiri a hasashen da ta yi game da kashe kwamandoji da tunzura ra'ayin jama'ar Iran don kifar da tsarin mulki, ya haifar da rikici a cikin ƙasashen da aka mamaye.
-
Iraki Ta Ayyana Ranar 30 GA Satumba A Matsayin Ranar Ƙarshe Ta Ficewar Dakarun Ƙasa Da Ƙasa
Iraki ta ayyana ranar 30 ga Satumba mai zuwa a matsayin ranar ƙarshe ta ƙarewar aiki da ficewar sojojin hadin gwiwar ƙasa da ƙasa daga ƙasarta.
-
Amurka Na Ci Gaba Da Kera Makaman Kakkabo Jigaren Marasa Matuka Na Iran A UAE
Amurka da kawayenta, waɗanda suka kasa maganin jiragen marasa matuki na Iran, sun koma ga kamfanonin fasaha don samun hanyar fuskantar ƙananan jirage marasa matuki masu arha amma masu ƙarfi na Iran; Kamfanin Amurka "Powerus," tare da kafa kamfanin samarwa a UAE, yana kera kusan makamai masu kakkabo jirage marasa matuki 3,000 a kowane wata, kuma yana ƙoƙarin ƙara samarwa zuwa 15,000 a kowane wata a tsakiyar shekara ta 2027.
-
Bunkasar Kasauwancin Turkiyya Ga Afirka Ya Kai Dala Biliyan 13.3
Fitar da kayyakin Turkiyya a kasashen Afirka a cikin watanni bakwai na farkon shekara ta 2026, tare da karuwar kashi 12.6 cikin dari idan aka kwatanta da lokaci guda na shekarar da ta gabata, ya kai dala biliyan 13.3, Masar, tare da karuwar kashi 49.3 cikin dari a watan Yuli, ta kasance kan gaba wajen shigo da kayayyaki daga Turkiyya a wannan nahiya.
-
Kanada Ta Kawo Ƙarshen Tattaunawarta Da Amurka
Firayim Ministan Kanada: Mun Kawo Karshen Tattaunawa da Amurka Saboda Ƙimar Da Suka Yi
-
Afghanistan: Fashewar Bam A Yankin Da 'Yan Shi'a Ke Rayuwa A Kabul
Wata fashewa sakamakon jefa gurneti ya faru a gidan burodi da ke gaban babban kanti na "Paywand" a Dasht-e-Barchi da ke yammacin Kabul.
-
Najeriya: Sama da Masallata 60 Ne Aka Sace
An sace masu salla sama da 60 a harin da wasu mutane dauke da makamai suka kai kan babban masallacin garin Dakara a jihar Neja ta Najeriya. Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da ake gudanar da sallar Juma'a, kuma maharan bayan sun yi ta harbe-harbe kwatsam, suka fitar da wasu masu salla daga masallacin suka tafi da su zuwa daji.