-
Jirgin Ruwa Mai Dauke Da 'Yan Gudun Hijira Rohingya Ya Kife, Ana Zulumin Mutuwar Mutane 500
An bayyana wannan hanyar a cikin Tekun Bengal a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin ruwa mafi haɗari a duniya ga 'yan gudun hijira da bakin haure.
-
Iran; Ta Aike Da Sako Ga Al'ummar Jordan
Iran: Ta Kai Hari A Kan Cibiyar Umarni Da Sarrafawa Ta Amurka A Jordan
Rundunar sararin samaniya ta dakarun juyin musulunci ta kai hari a kan sansanin Al-Azraq na Jordan da makamai masu linzami na "Khaibar Shikan," kuma ta yi kira ga al'ummar Jordan da su kai hari ga muradun Amurka yar mamaya su tsarkake ƙasarsu daga gare su.
-
Indiya Ta Hana Tura Ma'aikatan Ruwanta Kan Jiragen Ruwa Masu Wucewa Ta Mashigar Hurmuz
Indiya ta fitar da umarnin kada a tura ma'aikatan ruwa 'yan Indiya a kan jiragen ruwa da ke wucewa ta mashigar Hurmuz a cikin tashin hankali a yankin.
-
Najeriya: Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta Kwace Kadara 48 Ta Tsohon Ministan Shari'a
Wata kotu a Najeriya ta bayar da umarnin kwace kadarori 48 na tsohon ministan shari'a, kuma ta ce hukumar yaki da cin hanci tana zargin an siye su da kudaden da ba na doka ba.
-
Afirka Ta Kudu: Tawagar Tsaro Ta Musamman Ta Fara Bincike Kan Kisan Wani Shugaban Adawa
'Yan sandan Afirka ta Kudu suna bincike kan kisan wani shugaba a kungiyar "March and March" mai adawa da hijira, a cikin tashin hankali da barazanar da ke tattare da yakin korar bakin haure.
-
Iran: Ta Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Sufuri Tsakaninta Da Afganistan Da Tajikistan
An gudanar da taron bangarori uku na manyan jami'an kasashen Iran, Afganistan da Tajikistan a Mashhad, kuma a ƙarshe, bangarorin sun sanya hannu kan yarjejeniya don bude hanyar sufuri ta manyan motocin daukar kaya ta hadin gwiwa.
-
Iraqi: Mummunan Hatsari A Hanyar Tafiya Ta Arba'in Yayi Sanadin Mutuwar Mutane 8
Biyo bayan wani mummunan hatsari da ya faru a hanyar tafiyar tattakin Arba'in a Basra, maziyarta 'yan Iraki 8 sun mutu mutane 17 suka jikkata.
-
Hedkwatar Khatam: Idan Ku Harbi Ababen More Rayuwarmu, Duk Abubuwan More Rayuwa Da Ya Rage A Yankin Za Mu Kai Masu Hari
Mai Magana Da Yawun Hedikwatar Tsakiya Ta Khatam Al-Anbiya A Cikin Wani Gargadi Ga Makiya Ya Bayyana: Idan Ku Harbi Ababen More Rayuwarmu, Duk Abubuwan More Rayuwa Da Ya Rage A Yankin Za Mu Kai Masu Hari
-
Rahoto Cikin Hotuna | Zaman Makokin Matan Fatimiyya Ga Shahidin Jagora A Haramin Sayyidah Ma’asumah As Qom
Da safiyar yau Alhamis 25 Yuli, 2026 An gudanar taron tunawa da shahidin jagoran juyin juya hali na musamman ga mata, tare da jawabin Hujjatul-Islam Wal-Muslimin Sayyid Husain Momeni, a cikin dakin taro na wurin sallar Imam Khomeini (R.A) da ke haramin Hazrat Sayyidah Fatimah Ma’asumah (A.S).
-
Fakewa Da Wata Maslaha Da Takaita Hadafin Daukar Fansa, Bijirewa Umurnin Jagoran Juyin Juya Hali Ne
Ƙungiyar Malaman Makarantar Addini ta Qom ta jaddada cewa: A batun neman fansar jinin Imam Shahidi, duk wani neman maslaha ta duniya da takaita fannonin umarnin jagora masoyi na juyin juya hali, adawa da sabawa buƙatar al'umma da kuma bijirewa da umurnin jagoranci. عزاداری بانوان فاطمی در سوگ رهبر شهید انقلاب در حرم بانوی کرامت
-
Rahoto Cikin Hatuna | Na Taron Kasa Da Kasa Na Masu Isar Da Sakon Arba'in 1405
An gudanar da taron kasa da kasa na masu wa'azi da isar da sakon taron Arba'in na shekarar 2026 tare da karanta saƙon Ayatullahil-Uzma Subhani da jawaban wasu jami'an al'adu na ƙasar Iran, a safiyar yau Alhamis (16 Yuli, 2026) tare da halartar masu wa'azi da masu fafutuka na al'adu a fagen Arba'in, a Ofishin wakilin Waliyul Faqih a harkokin Hajji da Ziyara na Qom.
-
Farashin Man Fetur A Amurka Ya Kusa Kai Dala 4 A Kowace Galan / Girman Yaƙin Tattalin Arziki Ya Canja
Tashin hankalin tsakanin Amurka da Iran a Yammacin Asiya da abubuwan da ke faruwa a mashigar Hurmuz, sun ƙara farashin man fetur a Amurka da kashi 22% a cikin shekara ɗaya da ta gabata. Masana suna yin gargadin cewa a kwanaki masu zuwa, matsakaicin farashi a kowace galan na iya wuce dala 4. Ƙaruwar kuɗin makamashi ya kuma sake tayar da damuwa game da hauhawar farashi.
-
Al-Zaidi: Daga Satumba Ba Mu Buƙatar Kasancewar Wata Ƙungiya Mai Ɗauke Da Makamai A Ƙasar
Pentagon: Aikin Kawancen Kasa Da Kasa A Iraki Zai Kawo Ƙarshe
Ma'aikatar Yaƙi ta Amurka (Pentagon) a cikin wata sanarwa ta sanar da cewa aikin kawancen kasa da kasa a Iraki zai ƙare a ƙarshen watan Satumba. A lokaci guda, Ali al-Zaidi, firayim ministan Iraki, a ziyararsa zuwa Washington, ya jaddada cewa bayan 30 ga Satumba babu buƙatar kasancewar kowace ƙungiya mai ɗauke da makamai a Iraki, kuma sojojin tsaron wannan ƙasa suna da ikon kare dukkan ƙasar Iraki. Mai magana da yawun gwamnatin Iraki shi ma ya bayyana wannan ziyara a matsayin wani ɓangare na manufar haɓaka daidaitacciyar dangantakar kasashen waje bisa ga muradun juna.
-
An Ji Karar Fashewa Mai Ƙarfi A Herzliya A Arewacin Tel Aviv
An ji karar fashewa a kusa da wani wurin kasuwanci a yankin Herzliya
-
Zirga-zirgar Wucewa Ta Hanyar Kudu A Mashigar Hurmuz Ta Rage Zuwa Sifili
Kamfanin Kpler na kasa da kasa, wanda ya ƙware a nazarin bayanai game da kasuwannin makamashi, jigilar ruwa da kayayyaki masu muhimmanci, wanda ke da hedikwata a Belgium, ya ce zirga-zirgar wucewa ta hanyar kudu (wadda Washington ke iƙirarin tabbatar da ita) a mashigar Hurmuz ta ragu zuwa sifili.
-
Bidiyo | A Gaza Falasdinawa 15 Ne Su Kai Shahada A Cikin Sa'o'i 24 Bayan Harin Isra'ila
Isra’ila Na Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Akana Al’ummar Falasdinawa
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Taron Karawa Juna Sani Na Farkawar Musulunci Da Maɗaukin Tutar Gwagwarmaya
An gudanar da taron karawa juna sani mai taken "Farkawar Musulunci Da Maɗaukin Tutar Gwagwarmaya" bisa kulawar wakilin Waliyl Faqih da kuma shugaban kungiyar Ja'fariyya ta Pakistan, tare da halartar malamai da manyan 'yan Pakistan na makarantar addini ta Qom a ranar 14 ga Yuli, 2026, a dakin taro na Al-Ghadir.
-
Iraqi: Al-Zaidi Zai Je Iran A Mako Mai Zuwa
Majiyoyin yada labarai na Iraki sun ambata cewa firayim ministan Iraki, zai tafi Tehran a mako mai zuwa, bayan kammala ziyararsa ta yanzu a Washington.
-
Bidiyo | Yadda Makamai Masu Linzami 4 Suka Sauka Kan Sansanin Sojan Saman Malik Faisal A Jordan
Abin ban sha'awa a cikin wannan lamari shi ne, ba wai kawai makamai masu linzami na tsaro masu tsada sun kasa fuskantar makaman Iran ba, a'a, sai dai ma da alama daya daga cikin makaman ya lalata nau’rar tsaro da kansa, domin bayan harba shi, ba a sake harba wani makami na tsaro daga na’urar ba.
-
IRGC: Sun Babbake Cibiyar KJL Babban Tushe Na Kai Daukin Sojojin Amurka A Kuwait
Dakarun Juyin Musulunci: sun babbake KJL, babbar cibiyar shirya da tallafi na sojojin Amurka a Yammacin Asiya a Mina Abdullah na Kuwait.
-
IRGC: Ta Kai Munanan Hare-Hare Kan Muhimman Wuraren Amurka A Safiyar Yau
Dakarun Juyin Musulunci: Cibiyar Gudanarwa ta NSI, Cibiyar Sarrafa Kwamanda, Manyan ɗakunan ajiyar kayan aiki da kayan soji da tankokin man fetur na rundunar ruwa ta biyar ta Amurka a Bahrain an murkushe su.
-
Sheikh Zakzaky: Cimma Nasarar Addini Sadaukarwa Ya Ke Buƙata Ba Dabara Ba
Sheikh Zakzaky: Kashe Alamin Addini Yana Ƙara Tambatsa Addinin Ne
Cikin daren yau Talata 29 ga Almuharram 1448 (14/7/2026), Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da 'yan uwa almajiransa da suke karatu a Hauzozin Karbala mai tsarki a ƙasar Iraq.
-
Iran: Gwamnati Ta Sanar Da Daga Taron Tunawa Da Imam Shahidi (Qs) Zuwa Lahadi Mai Zuwa
Gwamnatin Iran a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa an jinkirta lokacin gudanar da taron tunawa da Imam Shahidin Juyin Juya Hali Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i (Allah Ya tsarkake ruhinsa), wanda za a gudanar da shi a ƙarƙashin kulawar rassan gwamnati uku na ƙasar, zuwa ranar Lahadi mai zuwa (19 ga Yuli), da karfe 10 na safe.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Taron Girmama Shahidin Jagoran Juyin Juya Hali A Filin Sallah Na Tehran
An gudanar da traon tunawa da Imam Mujahidi Shahidin jgaora bisa gayyatar Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene'i, jagora mai girma na juyin juya hali, da yammacin yau Laraba (14 Yuli, 2026) tare da halartar jami'an soji da farar hula da kuma dukkan al'ummar Tehran a farfajiyar filin sallah na Tehran.
-
Sojojin Yemen Sun Harba Jirgin Sama Leken Asirin Saudiyya A Tsakiyar Ƙasar
Yemen: Na Ci Gaba Da Ragargazar Saudiyya Da Makamai Masu Linzami
Amurka da gwamnatin yahudawa masu mamaya, saboda rashin iyawarsu wajen fuskantar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kawayenta a yankin, sun ba da umarni ga masarautun wahabiyawa a yankin da su shirya hare-hare a kan Iran da Yemen. Trump ya yi magana game da wannan a jawabinsa na jiya.
-
IRGC: Sun Babbake Sansanoni A Bahrain Da Kuwait A Cikin Zagaye Na Uku Na Aikin "Nasr 2"
Dakarun Juyin Musulunci na Iran sun sanar da aiwatar da hare-hare zagaye na uku na ayyukan "Nasr 2," hare-hare da suka kai a kan wuraren soji a Bahrain da Kuwait, sun tabbatar da lalata wasu ɗakunan ajiyar makamai da kuma lalata jirage mara matuki na makiya.
-
Yadda Zaman Majalisar Shurar Musulunci Iran Ya Kasance + Hotuna
An gudanar da zaman bayyane na Majalisar Shura ta Musulunci da yammacin ranar Litinin (13 ga Yuli,2026) tare da halartar wakilai 259, karkashin jagorancin Hamid Reza Haji Babaei, mataimakin shugaban majalisa, a ginin Baharistan.
-
Majalisar Iran: Wakilai 180 Sun Yi Kira Ga Neman Fansar Jini Da Kawo Ƙarshen Tattaunawa Da Amurka
Wakilai 180 na Iran sun buƙaci kawo ƙarshen fahimtar juna da Washington da kafa kwamitin majalisa don sake duba tattaunawar, suna bayyana niyyar amincewa da doka don sarrafa mashigar Hurmuz da tallafawa sojoji don neman fansar shahidai a matsayin martani ga sanarwar Trump na soke yarjejeniyar fahimtar juna.
-
Rasha Ta Yi Luguden Wuta Kan Kyiv Bayan Sanar Da Haɗin Kan Turai Don Taimakawa Ukraine
Rasha ta kai wani sabon hari da makamai masu linzami na ballastic a kan babban birnin Ukraine Kyiv, sa'o'i kadan bayan kasashe tara na Turai da Ukraine sun sanar da kafa haɗin gwiwa don haɓaka ƙarfin fuskantar makamai masu linzami na ballastic da kuma taimakon soji ga Ukraine.
-
Majalisar Ahlul-Bayt (A.S) A Kenya: Jagora Shahidi Ya Kare Musulunci Da Waɗanda Ake Zalunta Da Gwagwarmaya
Majalisar Ahlul-Bayt (A.S) a Kenya ta gudanar da taron tunawa da jagora shahidi Imam Khamene'i, a cibiyar Imam Ridha (A.S) a birnin Mombasa, tare da halartar wasu malamai da shugabannin addinai da sharifai da muminai daga sassan Kenya, inda mahalarta suka yaba da tafarkinsa wajen kare Musulunci da waɗanda ake zalunta, suna jaddada ci gaba da tafarkinsa wajen taimakon gaskiya da adalci.