-
Rahoton Amurka: Pentagon Da CENTCOM Suna Boye Bayanan Asarar Yaƙi Da Iran
Wani rahoto na gidan talabijin na ABC News ya bayyana cewa, Ma'aikatar Tsaro ta Amurka (Pentagon) da Cibiyar Rundunar Amurka (CENTCOM) suna gujewa buga kididdigar da aka sabunta game da asarar yaƙi da Iran, a cikin tambayoyi game da daidaiton alkaluman hukuma da aka bayar.
-
Reuters: An Samu Raguwar Dakon Man Fetur Bayan Takunkuman Yamen Akan Saudiyya
Reuters: An Samu Raguwar Ayyukan Dako Da Ɗora Danyen Man Fetur Daga Tashar Jiragen Ruwa Ta Yanbu Na Saudiyya Bayan Sanar Da Takunkumin Yamen A Kan Saudiyya
-
Sojojin Yemen Sun Kai Hari A Kan Jirgin Ruwan Dakon Man Fetur Na Saudiyya Da Tilasta Shi Ja Da Baya
Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da wani aikin soji wanda ya kai hari a kan jirgin ruwan dakon man fetur na Saudiyya "NCC GHAZAL," suna tabbatar da cewa, jirgin ya keta dokar hana zirga-zirgar ruwa da aka sanya wa Saudiyya, kuma ya ƙi amsa kiran gargadi.
-
Cikin Bidiyo | Miliyoyin Maziyarta Arba’een Suna Kwarara Zuwa Karbala Domin Ziyarar Arba'in
Cikin Bidiyo | Miliyoyin Maziyarta Arba’een Suna Kwarara Zuwa Karbala Domin Ziyarar Arba'in
-
Kaitsaye: Sojojin Mamaya Sun Kai Hari Da Bama-bamai A Garuruwa Uku A Kudancin Lebanon
Sojojin Mamaya Sun Kai Hari Da Bama-bamai A Garin Kafr Tibnit A Kudancin Lebanon Sannan Sun Kai Hari Da Bama-bamai A Garin Zutar Al-Sharqiyyah A Kudancin Lebanon. Har wala Yau Sojojin Mamaya Sun Kai Hari Da Bama-bamai A Gefen Garin Al-Qantarah A Kudancin Lebanon
-
Reuters: Oman Ta Gabatar Da Shirin Yanki Ga Iran Don Sarrafa Mashigar Hurmuz Tare
Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya nakalto daga wata majiya a yankin Tekun Farisa rahoton cewa, Oman ta gabatar wa Iran wata shawara, tare da goyon bayan wasu kasashen yankin, don samar da wata hanya ta hadin gwiwa wajen sarrafa mashigar Hurmuz; shirin da bisa gare shi, masu amfani da wannan hanyar ruwa za su biya kuɗin ayyukan jigilar ruwa da yadda suke so.
-
FT: Iran Ta Ƙara Dagula Ma'aunin Amurka Da Isra'ila Ta Hanyar Sake Gina Ƙarfin Makamanta Masu Linzami
Jaridar Ingila Financial Times, a cikin wani rahoto tana mai nuni ga ayyukan Iran a 'yan watannin da suka gabata, ta rubuta cewa, Jamhuriyar Musulunci, duk da hare-hare masu yawa, ta sami nasarar kiyaye ƙarfin makamanta masu linzami, kuma ta hanyar sake gina ƙarfin sojinta cikin sauri, ta ƙara dagula ma'aunin Amurka da gwamnatin yahudawa.
-
Iran: Ta Aike da Ma'aikatan Lafiya 300 Daga Fars Zuwa Dakunan Lafiya A Hanyar Tattakin Arba'in
Shugaban rundunar lafiya ta al'umma a lardin Fars ya ba da rahoton aika ma'aikatan lafiya 300 daga Jami'ar Kimiyyar Lafiya ta Shiraz zuwa Iraki, kuma ya ce: Waɗannan ma'aikata, a cikin dakunan lafiya 11 da aka girka a hanyar tattakinArba'in, suna ba da ayyukan lafiya, kulawa da agaji ga maziyartan Husaini a kowane dare da rana.
-
Labarai Cikin Hotuna | Dunƙulanlun Hannayen Maziyartan Arba'in A Kan Masu Girman Kai Na Duniya
Maukibin haramin Hazrat Fatimah Ma’asumah (A.S) da ke runfa ta 1080 kan hanyar tafiya daga Najaf zuwa Karbala, a matsayin ɗaya daga cikin haramai na Uwa Karimiya, yana karbar bakuncin taron masu adawa da masu girman kai, kuma maziyartan Arba'in, tare da dunƙulallun hannaye da shelanta "Mutuwa ga Amurka," suna masu nuna ƙin yarda ga masu girman kai na duniya.
-
Iran: Zamu Rufe Fayil Din Isra’la Na Har Abada
Aref: Sake Farwar Yaƙi Da Yahudawa Yana Nufin Kawo Ƙarshen Su Na Har Abada
-
Ƙungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam Sun Yi Allah Wadai Da Korar Ma'aikata 'Yan Shi'a Daga UAE
Ƙungiyar kare hakkin dan adam ta Equidem, da ke Landan, ta sanar da cewa, korar ma'aikata 'yan ci-rani da yawa, musamman 'yan Shi'ar Pakistan, daga Hadaddiyar Daular Larabawa, ta kasance tare da zarge-zarge kamar "ƙirƙirar shari'a bisa ga mazhaba," kamewa ba tare da izini ba, hana biyan albashi, da kuma keta tsarin shari'a; dukkan mutanen da wannan hukuma ta yi hira da su, sun ce, bayan halartar masallacin Shi'a da kuma rubuta bayanan su, an kama su kuma an kore su.
-
Politico: Ganawar Netanyahu Da Trump Musiba Ce Ne Ga 'Yan Kungiyar America First
Ganawar Benjamin Netanyahu da Donald Trump ta haifar da tashin hankali a tsakanin masu ra'ayin mazan jiya na jam'iyyar Republican; domin sun yi imanin cewa Netanyahu, don ceto rayuwarsa ta siyasa, yana ƙoƙarin jawo Amurka cikin tarkon yaƙi da Iran.
-
Iran: Duk Wata Ƙasa Da Ta Yi Amfani Da Dukiyoyin Iran, Ba Za Ta Sami Izinin Wucewa Ta Mashigar Hormuz Ba
Mai magana da yawun hedikwatar Khatamul-Anbiya ya yi gargadin cewa, duk wani kamfani ko ƙasa da ta karɓi wani kuɗi daga dukiyoyin Iran, ba za ta sami izinin wucewa ta mashigar ba.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Yadda Maziyarta 'Yan Iran Suke Halartar Tattakin Arba'in A Hanyar Najaf Da Karbala
Hanyar Karbala mai tsarki da Najaf Ashraf suna shaida kasancewar maziyarta 'yan Iran na musamman, suna ɗauke da hotunan Shahid Imam Sayyid "Ali Khamene'i" da tutocin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
-
Labarai Cikin Bidiyo | Yadda Sojojin Yemen Suka Kakkabo Jirgin Yaƙi "Bayraktar" Saudiyya
Kafofin yada labaran yaƙi sun watsa hotunan harbowa da tarkacen jirgin sa ido mai ɗauke da makamai na makiya Saudiyya, wanda sojojin Yemen suka harba a yau, a lokacin da yake gudanar da ayyukan liken asiri a sararin lardin Al-Jawf. Hotunan sun nuna tsarin sa ido da bin jirgin "Bayraktar Akinci" na ƙasar Turkiyya, da lokacin faɗuwarsa, baya ga hotunan tarkacen jirgin yana ci da wuta bayan faɗuwar sa a ƙasa. Kuma jirgin "Bayraktar" jirgi ne mara matuki na yaƙi mai muhimmanci daga nau'in masu tsayi da dogon zango, kuma an kera shi ne musamman don aiwatar da ayyukan kai hari na dabaru waɗanda a baya suka keɓanta ga jiragen yaƙi na gargajiya masu matuki kamar "F-16."
-
Rahoto Cikin Hotuna | Bayar da gudunmawar Ayyukan Al'adu Na Mata Ga Maziyartan Arba'in
Laburaren mata na Ummul-Banin (A.S) ya fara bayar da ayyukansa na al'adu ga maziyarta Arba'in a rukunin Ummul-Banin (A.S). Ayyukan sun haɗa da shirya baje kolin littattafai wanda ya ƙunshi tarin littafan addini, al'adu da ilimi daban-daban, tare da littattafai na musamman kan harkokin mata da yara, wanda ke ba maziyarta damar duba tushen ilimi daban-daban waɗanda ke wadatar da ƙwarewarsu ta al'adu yayin ziyara.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Hidimtawa A Dare Da Rana Ga Maziyartan Arba'in Na Husaini A Ilam
A daidai lokacin da aka fara kwararar maziyartan Arba'in na Imam Husaini da ƙaruwar zirga-zirgar su daga iyakokin yammacin ƙasar, lardin Ilam, a matsayin ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin da ke kaiwa wuraren ibada masu tsarki, yana karbar bakuncin dubban maziyarta na cikin gida da waje. A wannan tsari, ayukan masoya Amiril-Mu'minin (A.S), tare da haɗin gwiwar Gidauniyar Marasa Ƙarfi ta Juyin Juya Hali, suna ba da ayyuka na jin daɗi da walwala, wurin kwana, karɓar baƙi, tsaftace kaya, lafiya, banki, da shirye-shiryen al'adu da addini ga maziyartar Arba'in a kowane dare da rana.
-
Yadda Sanya Takunkuman Makamai Na Kasashen Duniya Ya Gurgunta Da Illatawa Kan Ayyukan Yaƙin Isra’ila
Takunkuman kasashen duniya a cikin samar da makamai, kayan gyara da albarkatun ƙasa, sun zama barazana ta aiki ga sojojin gwamnatin yahudawa.
-
Ansarullah: Sojojin Yemen Sun Ƙara Ƙarfin Makamai Masu Linzami Na Musamman
Wani babban jami'in Ansarullah a Sana'a ya ce sojojin sun ƙara ƙarfin makamai masu linzami na musamman a kwanan nan ga makamansu waɗanda Yemen kaɗai ke da su.
-
Isra'ila Na Ci Gaba Da Kai Hare-Hare A Kudancin Lebanon, Tana Kona Da Rushe Gidaje A Bint Jbeil
Sojojin mamaya na "Isra'ila" sun kai hare-hare masu yawa a kudancin Lebanon a ranar Asabar, ciki har da kona da rushe gidaje a yankin Bint Jbeil, yayin da hukumomin siyasar Lebanon ke ci gaba da tattaunawa kai tsaye da "Isra'ila" ƙarƙashin jagorancin Amurka kan abin da ake kira "Tsararriyar Yarjejeniyar."
-
Haramin Sayyid Abbas Ya Buɗe Mawkibin Al'adu na Baiɗaya A Cikin Rukunin Ummul-Baneen Domin Hidimatawa Masu Ziyara + Hotuna
Haramin Al-Abbas (a.s) mai tsarki ya buɗe Maukibin al'adu na Baiɗaya a kan hanyar mahalarta ziyara a kan titin (Karbala - Najaf), a cikin rukunin Ummul-Baneen (amincin Allah ya tabbata a gare ta) domin hidimawa mahalarta ziyara, a daidai lokacin da mahalarta ziyara ke kwararowa don tunawa da Ziyarar Arba'in.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Haramin Imam Ridha As Ya Aike Da Kunshin Abinci 150,000 Ga Mahalarta Ziyarar Arba'in
Kamfanin dillancin labarai na Ahl al-Bayt: Ta hanyar ƙoƙarin Gidauniyar Razavi Dignity, an aika kunshin abinci 150, daga Kamfanin Masana'antar Abinci na haramin Imam Ali Ridha As domin mahalarta ziyarar Arba'in a ranar Alhamis, 23 ga Yuli, 2026.
-
Sakon Jagora Ga Hizbullah
Jagora Sayyid Mujtaba Khamene'i: Kare Mujahidan Lebanon, Siyasar Dabaru Ce Ta Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
Jagoran juyin juya halin Musulunci, a cikin wani sako, sun jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran, a cikin manufar siyasar jagora shahidi, ta sanya kare waɗannan mujahidai masu ƙarfi da ake zalunta a matsayin muhimmiyar manufar dabaru.
-
Manazarcin Tsaro Kuma Masanin Harkokin Bayanai:
Nazari: CIA Tana Aiki Ne Ga Isra'ila, Ba Don Amurka Ba
John Kiriakou, manazarcin tsaro kuma masanin harkokin bayanan sirri, yana mai suka mai tsanani game da yanayin da CIA ke ciki a yanzu, ya yi iƙirarin cewa wannan hukuma ta shiga cikin tasirin ƙungiyoyin yahudawa sosai, kuma maimakon ta ci gaba da anfanar manufofin ƙasar Amurka, tana aiki ne don cimma manufofin Isra'ila.
-
UNOCHA: Karancin Kasafin Kuɗi Yana Barazana Ga Ayyukan Ciwarwa Ga Yara Da Mata Miliyan 5.7 A Afganistan
Ofishin Gudanar da Taimakon Bil'adama na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargadin cewa, karancin albarkatun kuɗi ya sanya samun damar yara da mata miliyan 5.7 a Afganistan ga ayyukan lafiya da abinci na yau da kullun cikin hadari mai tsanani.
-
MDD: Ta Jaddada Buƙatar Ɗaukar Matakin Gaggawa Don Tallafawa Mata Da 'Yan Mata Na Afganistan
Shugaban ofishin sashen mata na Majalisar Ɗinkin Duniya, a ziyararsa zuwa Afganistan, ya tattauna da jami'an Taliban da abokan huldar diflomasiyya game da ƙara tallafawa mata da 'yan mata, da kuma cire ƙuntatawa da aka sanya wa ma'aikatan mata na hukumomin jin kai.
-
Tonon Silili Yadda 'Yan Ƙasar Italiya Kusan 1,000 Su Kai Tarayya A Kisan Kiyashin Gaza
Hannun Kasar Italiya Dumu-Dumu A Kisan Kiyashin Da Isra’ila Ke Yiwa Falasdinawa
Bayanan hukumar ma'aikatar yaƙi na gwamnatin yahudawa da aka buga kwanan nan, sun nuna cewa 'yan ƙasar Italiya 928 sun shiga cikin kisan kiyashin da Isra’ila k yi a zirin Gaza daga Oktoba 2023 zuwa Maris 2025. Bayyana waɗannan takardun, waɗanda ke nuna haɗin gwiwar Rome da Tel Aviv fiye da dangantakar hukuma, ya haifar da cece-kuce mai yawa a cikin muhawarru na siyasa na Italiya, kuma Stefania Ascari, 'yar majalisar Italiya, ta zargi gwamnatin ƙasarta da gujewa daukar alhakin hakan.
-
Al Khalifa Da Yaƙi Da Al'amuran Addini; 'Yan Shi'a Ba Sa Mika Wuya A Tarihi
Bahrain, a gab da lokutan tarukan addini, ta sake fuskantar ƙuntatawa na gwamnati a kan al'amuran addini na 'yan Shi'a; ƙuntatawa waɗanda, a ganin masu lura, sun wuce iyakar da aka "tsara" kuma sun zama fagen sarrafawa da takaita ayyukan addini. Duk da haka, shaidun tarihi da zamantakewa sun nuna cewa al'ummar Shi'a ta Bahrain na ci gaba da tabbatuwa da kiyaye asalin addini da al'amuran Imam Husaini As.
-
Bahrain: Hanawar Hukuma Ga Halartar Arba’een Bai Hana Su Nuna Bakin Cikinsu Ba Ga Shahadar Imam Husain As
Yayin da Arba'in na Hussaini ke gabatowa, hana 'yan Shi'a na Bahrain tafiya zuwa wuraren ibada masu tsarki, ya haifar da kwararar bayyana ƙaunar da baƙin ciki a tsakaninsu; dubban 'yan Bahrain waɗanda kowace shekara sukan isa Karbala, a wannan shekara, saboda haramcin tafiyar a hukumance, sun yi tafiya zuwa Arba'in da zukatansu kawai.
-
Yahudawa Na Kai Harin Dabbancin Kan Fursunonin Matan Falasdinu A Kurkukun Al-Damun
Cibiyoyin kula da al'amuran fursunonin Falasdinu a yau (Lahadi) sun ba da rahoton faruwar wani aikin danniya mai tsanani a kan fursunonin mata na Falasdinu a kurkukun Al-Damun. Dangane da wannan rahoto, sojojin gwamnatin mamaya, ta hanyar kutsawa sashen mata a tsakiyar daren Juma'a, ta amfani da hayaki mai sa hawaye, duka da wulakanci, sun haifar da shaƙewar numfashi da kuma tsananta yanayin raunin jiki na wasu daga cikinsu. A halin yanzu, mata 94 na Falasdinu, ciki har da mata biyu masu juna biyu da marasa lafiya biyu masu ciwon daji, suna cikin wannan kurkuku.