-
Isra'ila Na Ci Gaba Da Kai Hari A Labenon
Isra'ila na Ci Gaba da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Ta Ayyukan Jefa Bama-bamai Da Kutsawa A Kudancin Labanon
-
A Lebanon Mutuwa Ba Ta Zama Mafaka Ba; Isra’ila Ta Kai Harin Bama-bamai a Makabartun Kudancin Lebanon
Hare-haren bama-bamai na gwamnatin yahudawa a kudancin Lebanon ba wai kawai sun takaita ga lalata gidaje da hanyoyi da gonaki ba, har ma sun kai hari ga makabartu.
-
Rahoto Cikin Bidiyo | Haska Tehran Daga Sama Yayin Sallar Jana'iza A Kan Shahid Imam Khamene'i (R.A) A Filin Sallah Na Imam Khomeini (R.A)
Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA - An dauki hoton filin sallah na Imam Khomeini (R.A) daga sama yayin gudanar da sallar jana'iza a kan Shahid Imam Khamene'i (R.A).
-
Shahadar Jariri A Yammacin Ramallah Bayan Mamaya Ya Hana Kai Shi Asibiti
Majiyoyin lafiya a yau Lahadi, sun tabbatar shahadar wani jariri sakamakon hanawar da sojojin mamaya don kai shi jinya ta ƙofar Deir Ammar da ke yammacin birnin Ramallah wadda aka rufe tun watanni 5 da suka gabata.
-
An Yi Sallar Jana'iza A Kan Gawarwakin Imam Shahidi Da Iyalinsa Da Imamancin Ayatullah Subhani
An gudanar da salloli uku; na farko a kan gawar Imam Shahidin Al'umma, na biyu a kan gawarwakin shahidai Misbahul-Huda Baqeri-Kani, Zahra Haddad Adel, da Hajiya Bushra Al-Khamene'i, yayin da aka gudanar da sallah ta uku a kan gawar shahida Zahra Mohammadi Gulfaigani.
-
Bidiyo Da Hotunan Yadda Aka Gabatar Da Sallah Ga Gawar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci
An gabatar da sallar jana'izar Shahidin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Sayyid Imam Ali Alkhameni Qs a Masallacin Mosallah Imam Khomeini a Tehran, inda Ayatullah Subhani ya jagoranci sallar tare da halartar milyoyin Al'umma.
-
Sojojin Lebanon Sun Kwance Wasu Bamamai Na Isra’ila Da Ba Su Fashe Ba
Sojojin Lebanon sun ba da rahoton kwance wasu bama-bamai guda huɗu da ba su fashe ba daga hare-haren gwamnatin yahudawa a kudancin ƙasar.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Halartar Mililyoyin Al’umma Taron Bankwana Da Jagora Shahidin Juyin Juya Hali - 4
An fara taron bankwana da Shahid Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i (R.A) da iyalinsa, daga safiyar jiya Asabar (04 Yuli, 2026) wanda ya je gudana yar yanzu tare da halartar miliyoyin mutane masu makoki a filin sallah na Tehran. Shahidin Iran ya sami darajar shahada a ranar Asabar 9 ga Isfand, 1405HS wanda yayi daidai da 10 ga Ramadan 1447HQ wanda ya dace da 28, February 2026M a yayin wani harin ta'addanci na magunyar Amurka da Isra’ila
-
Iraki: An Jibge Sojojin Hashdush-Sha'abi 30,000 Don Tabbatar Da Tsaron Jana'izar Shahidin Jagora A Najaf Da Karbala
Rundunar Hashdush-Sha'abi ta Iraki a yankin Furat ta Tsakiya, tare da hadin gwiwar kwamandancin ayyukan hadin gwiwa na sojojin Iraki, ta ajiye sojojinta 30,000 tun daga safiyar yau a garuruwan Najaf, Karbala da yankunan da ke kewaye, don tabbatar da tsaron jana'izar da bankwana da gawar shahidin jagora juyin juya halin Musulunci.
-
An Rufe Ofisoshin Gwamnati Da Gudanar da Tsari Na Musamman Don Jana'izar
Lardin Babil Iraki Yana Shirye-shiryen Jana'izar Shahid Ayatullah Khamene'i
Majalisar Lardin Babil Iraki, tare da gudanar da taron gaggawa a gab da jana'izar gawar Shahid Ayatullahil-Uzma Sayyid Ali Khamene'i, ta ayyana ranakun Laraba da Alhamis a matsayin ranakun hutu a wannan lardin.
-
Labarai Cikin Hotuna | Na Taron "Imam Khamene'i; Jagoran Gwagwarmaya Na Har Abada"
Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Tawagogi daga Majalisar Malaman Shi'a na kasashen duniya da wasu malamai da manyan 'yan Shi'a, tare da shugabanni da masana na duniyar Musulunci da shugabannin fagen gwagwarmaya, sun halarci wannan taron na kasa da kasa mai taken "Imam Khamene'i; Jagoran Gwagwarmaya Na Har Abada." An gudanar da wannan taron a ranar Asabar 04 Yuli a dakin taron shugabannin Tehran tare da halartar shugaban ƙasa mai girma.
-
Sojojin Yahudawa Sun Kai Hare-Hare A Yankuna Daban-Daban Na Yammacin Kogin Jordan
Majiyoyin cikin gida sun ba da rahoton yawaitar hare-haren sojojin gwamnatin yahudawa da hare-haren mazauna yahudawa a yankuna daban-daban na Yammacin Kogin Jordan.
-
UNOCHA: Hare-Haren Pakistan A Afganistan; Sun Dagula Rayuwa Da Hankalin Yara
Ofishin Gudanar da Taimakon Bil'adama na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNOCHA) ya jaddada cewa bai kamata fararen hula su biya bashin yaƙe-yaƙe da rikice-rikice ba, kuma dukkan bangarorin da ke rikici suna da alhakin kare su bisa ga dokokin jin kai na kasa da kasa.
-
Isra’ila Ta Yaye Kallabin Hadin Gwiwar Tsaronta Da UAE A Yaƙinta Da Iran
Ministan Sufuri na gwamnatin yahudawa a karon farko a hukumance ya bayyana cewa a yayin yaƙin baya-bayan nan da Iran, Tel Aviv ta aika da wata na’urar tsarin tsaron sama "Kubbar Karfe" zuwa UAE, kuma ta tura wasu sojojinta zuwa ƙasar UAE don gudanar da wannan na’urar.
-
Labarai Cikin Hotuna | Halartar Majalisar Malaman Shi'a Ta Afganistan A Taron "Imam Khamene'i; Jagoran Gwagwarmaya Na Har Abada"
Labarai Cikin Hotuna | Halartar Majalisar Malaman Shi'a Ta Afganistan A Taron "Imam Khamene'i; Jagoran Gwagwarmaya Na Har Abada"
-
Pakistan Ta Gudanar da Taro Na Ilimi Kan Manufar Karbala A Mahangar Shahidin Jagora + Hotuna
An gudanar da wani taro karawa juna sani da jajantawa mai taken "Manufar Karbala A Mahangar Shahidin Jagora" a ƙarƙashin jagorancin Allamah Maqsud Ali Dumaki a Jacobabad, Pakistan.
-
Labarai Cikin Hotuna | Na Ganawar Araghchi Da Tawagar Hizbullah Bayan Halartar Jana'izar Imam Khamene'i
Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya gana da tawagar Hizbullah da ta halarci tarukan jana'izar shahidi Imam Sayyid Ali Khamene'i.
-
Mashigar Hurmuz: Daga Hanyar Makamashi Zuwa Kayan Aikin Fuskantar Makiya Iran
Yaƙin kwanaki 40 ba wai kawai arangamar soji ce tsakanin Iran da makiya ba; harma ta zama wurin juyi na canza ma'aunin iko a Tekun Farisa da kuma sake fasalin manufar fuskantar makiya a yammacin Asiya.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Halartar Mililyoyin Al’umma Taron Bankwana Da Jagora Shahidin Juyin Juya Hali - 3
An fara taron bankwana da Shahid Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i (R.A) da iyalinsa, daga safiyar yau Asabar (04 Yuli, 2026) tare da halartar miliyoyin mutane masu makoki a filin sallah na Tehran. Shahidin Iran ya sami darajar shahada a ranar Asabar 9 ga Isfand, 1405HS wanda yayi daidai da 10 ga Ramadan 1447HQ wanda ya dace da 28, February 2026M a yayin wani harin ta'addanci na magunyar Amurka da Isra’ila. …………………….
-
Iraki: Ta Ƙaddamar da Jiragen Kasa Na Musamman A Kan Hanyar Basra - Karbala Domin Jana'izar Shahidin Jagora
Kamfanin Jirgin Kasa na Iraki ya keɓe jiragen kasa na musamman don jigilar masu makoki na jana'izar Shahid Ayatullahil-Uzma Sayyid Ali Khamene'I Rh a Iraki.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Halartar Mililyoyin Al’umma Taron Bankwana Da Jagora Shahidin Juyin Juya Hali - 2
An fara taron bankwana da Shahid Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i (R.A) da iyalinsa, daga safiyar yau Asabar (04 Yuli, 2026) tare da halartar miliyoyin mutane masu makoki a filin sallah na Tehran. Shahidin Iran ya sami darajar shahada a ranar Asabar 9 ga Isfand, 1405HS wanda yayi daidai da 10 ga Ramadan 1447HQ wanda ya dace da 28, February 2026M a yayin wani harin ta'addanci na magunyar Amurka da Isra’ila.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Halartar Mililyoyin Al’umma Taron Bankwana Da Jagora Shahidin Juyin Juya Hali - 1
An fara taron bankwana da Shahid Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i (R.A) da iyalinsa, daga safiyar yau Asabar (04 Yuli,2026) tare da halartar miliyoyin mutane masu makoki a filin sallah na Tehran. Shahidin Iran ya sami darajar shahada a ranar Asabar 9 ga Isfand, 1405HS wanda yayi daidai da 10 ga Ramadan 1447HQ wanda ya dace da 28, February 2026M a yayin wani harin ta'addanci na magunyar Amurka da Isra’ila.
-
Yadda Kafofin Yada Labaran Larabci Suka Yada Tarukan Bankwana Da Shahidin Jagoran Musulunci
Kafofin yada labarai na duniyar Larabawa tun daga Yemen da Lebanon zuwa Iraki da Qatar, sun gudanar da cikakken rahoto kaitsaye na taron bankwana da jana'izar shahidin jagoran juyin juya hali, tare da bayyana wannan taro a matsayin "Jana'izar Ƙarni," sun haskaka halartar miliyoyin mutane, sakonnin tsayin daka da kasancewar kwamitocin kasashen waje daga kusan kasashe 100, kuma sun ɗauki shi a matsayin alamar ci gaba da hanyar juyin juya halin Musulunci da kuma jigon gwagwarmaya.
-
The Independent: An Shirya Tsare-Tsare Masu Yawa Don Jana'izar Gawar Shahidin Jagoran Iran
Jaridar Ingila The Independent a cikin wani rahoto, yayin da take yin nuni ga fara tarukan tunawa da jana'izar gawar Ayatullahil-Uzma Sayyid Ali Khamene'i, Shahidin jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta ba da rahoton tsare-tsare masu yawa na tsaro, zirga-zirga da takaita sararin samaniyar Tehran don gudanar da wannan taron na ƙasa, kuma ta rubuta cewa an dakatar da ayyukan yau da kullun a babban birnin.
-
Jami'an Kasashe Waje Sun Isar Da Juyayin Shahadar Jagoran Juyin Juya Hali Ga Al'ummar Iran Na
Ganawar Ministan HW Iran Da Jami'an Kasashe Duniya Daban-Daban A Tehran
Jami'an kasashe daban-daban na duniya da suka yi tafiya zuwa Tehran don halartar taron jana'izar shahidin jagoran juyin juya halin Musulunci, sun gana da Sayyid Abbas Araghchi, Ministan Harkokin Wajen Iran, tare da yin tattaunawa, kuma sun isar da sakonnin juyayi da hadin kai ga gwamnati da al'ummar Iran, tare da jaddada shirye-shiryensu don haɓaka dangantaka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
-
Kwamandan Sojojin Ruwa IRGC: Ɗaukar Fansar Allah Na Gaba Da Tabbata Akan Amurka Da Isra'ila
A yau, muna jimamin rasuwar wani babban mutum wanda yayi shahada a hannun mafi mugunyar mutane da mafi fasikanci a doron ƙasa; makafin mutane da suka ji tsoron ikonsa na ruhaniya, da ƙarfin fasaharsa, da zurfin tunaninsa, saboda ba su iya jurewa hasken imaninsa da basirarsa ba, suka aikata wannan mummunan laifi. Ya kamata waɗannan 'yan Kurdawan masu girman kai da mabiyansu da aka horar da su su sani cewa da wannan mugun aikin bai iya haifar da cikas a tafarkin gaskiya...
-
Rahoto Cikin Hotona | Yadda Aka Gudanar da Taron Alamta Jana'izar Gawar Imam Shahidi A Najeriya
Rahoto Cikin Hotona | Yadda Aka Gudanar da Taron Alamta Jana'izar Gawar Imam Shahidi A Najeriya
-
Rasha Ta Kakkabo Jirage Marasa Matuki 40 N Ukraine Da Suka Nufi Shiga Moscow A Cikin Sa'o'i 24
Shugaban babban birnin Rasha Sergei Sobyanin ya sanar da cewa tsarin tsaron saman kasar ya sauke tare da lalata jirage marasa matuki 40 da suka nufi shiga Moscow a cikin sa'o'i 24.
-
Cikakken Rahoto Na Yadda Al'umma Suke Bankwana Na Tarihi Ga Shahidin Jagoran Juyin Juya Hali A Filin Sallah Na Tehran + Bidiyo Da Hotuna
Tun daga safiyar yau an buɗe ƙofofin filin sallah na Tehran ga al'umma masu nuna makoki da masu neman fansar jinin Imam Shahidi, don fara rana ta biyu na shirye-shiryen bankwana da jana'izar, da kuma rana ta farko na bankwana na al'umma da Imaminsu.
-
Grossi: Babu Takamaiman Ranar Shigar Da Masu Binciken Hukumar Cikin Wuraren Nukliyar Iran
Biyo bayan hare-haren Amurka a kan wuraren nukiliyar Iran a watan Yuni 2025, Iran ta takaita hadin gwiwarta da Hukumar Makamashi ta Duniya da kuma damar shiga wuraren nukiliya, tana mai tabbatar da cewa dukkan shawarwarin da suka shafi mu'amala da hukumar suna cikin ikon majalisar koli ta tsaron ƙasa ta Iran.