-
Rahoto Cikin Hotuna Na Ganawar Sheikh Ibrahim Zakzaky Hf Da Ɗalibai Da Suka Haddace Alkur'ani
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ɗalibai daga makarantun fudiyya daban daban dake shirin bikin hardace Alkur’ani sun ziyarci Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), yau Laraba a gidansa dake Abuja.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Bikin Maulidin Ma'asumah (a.s) A Haramin Sayyid Abbas (a.s).
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: tare da halartar 'yan shi'a na kasar Iraki, an gudanar da bukukuwan maulidin Sayyida Fatima Ma'asumah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta a farfajiyar haramin atabatul Abbas (A.S).
-
Labarai Cikin Hotuna Na Ziyarar Sheikh "Ibrahim Zakzaky" Zuwa Haramin Imamain Kazimain (AS)
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Sheikh "Ibrahim Zakzaky Hf Babban shugaban Harkar Musulunci a Nigeria, a cikin tafiyarsa kasar Iraki da ci gaba da kai ziyarorin da yake yi ya samu karramawa da tagomashin ziyarar Haramin Imamain Kazimain (a.s.) da ke birnin Bagadaza Irak
-
Sheikh Ibrahim Zakzaky Hf: "Ba Wa'azi Zakuyi Ba, Karantarwa Zakuyi, Meye Aikin Ku? Karatu! Don Kuyi Me?, Karantarwa".
"Ba Wa'azi Zakuyi Ba, Karantarwa Zakuyi, Meye Aikin Ku? Karatu! Don Kuyi Me?, Karantarwa".
-
Labarai Cikin Hotuna Na Yadda Birnin Khan Yunus Ya Koma Bayan Janyewar Dakarun Yahudawan Sahyuniyawa
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: wadannan hotuna na nuni da irin barnar da dakarun yahudawan sahyuniya suka yi a garin Khan Yunus na zirin Gaza bayan hare-haren da suka kai ta sama da ta kasa wanda yanzu suka janye daga birnin inda suka bar birnin a rushe kakaf.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Yadda Falasdinawa Suke Yin Hijira Daga Gabashin Birnin Rafah Bayan Sanarwar Isra'ila Na Kai Hari
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya bayar da rahoton cewa: bayan sanarwar da sojojin yahudawan sahyoniyawan suka yi na kauracewa wasu unguwanni a gabashin Rafah da ke kudancin zirin Gaza, Palasdinawa mazauna wannan yanki sun fara ficewa daga yankin da wuraren su.
-
Rahoto Cikin Hatuna Na Gudanar Da Zaman Makokin Shahadar Imam Sadik (A.S.) A Lambun Shahidan Ali Bin Jafar (A.S.) Da Ke Birnin Kum.
Kamfanin dillancin labaran na kasa da kasa na Ahlul-Bait (A.S) ya kawo maku rahoton cewa: an gudanar da zaman juyayin shahadar Imam Jafar Sadik (a.s.) tare da jawabin "Hujjatul Islam Wal muslimiin "Mahdi Daneshmand" da kuma waken juyayi daga Hajji Syed Mahdi Mirdamad" a Gulzar Shahada Ali bin Jafar (a.s.) a birnin Qum. Hoto: Hadi Cheharghani
-
Rahoto Cikin Hatuna Na Gudanar Da Zaman Makokin Shahadar Imam Sadik (A.S.) A Husainiyar Imam Amirul Muminin (A.S.) A Birnin Isfahan.
Kamfanin dillancin labaran na kasa da kasa na Ahlul-Bait (A.S) ya kawo maku rahoton cewa: an gudanar da zaman makokin shahadar Imam Sadik (a.s.) a Husainiyar Imam Amirul Muminin (A.S.) Isfahan (a.s) in da ya samu halartar mutane daban-daban.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Halartar Shugaban Majalisar Ahlul-Bait (AS) A Makarantar Hauzar Curitiba Kasar Brazil.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (A.S) wanda ya samu gayyata daga musulmin Brazil domin halartar taro mai taken "Musulunci Addinin Rayuwa Da Tattaunawa Ne" ya isa zuwa wannan kasa, a gefen wannan tafiya, inda ya halarci makarantar hauza ta Curitiba, Brazil, kuma ya ba da jawabi ga ɗaliban wannan makarantar hauza.
-
Hoto: Hadi Cheharghani
Rahoto Cikin Hotuna Na Halartar Babban Shuagaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) A Masallacin Sayyidina Ali bin Abi Talib (AS) Da Ke Curitiba A Kasar Brazil.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (A.S) wanda ya samu gayyata daga musulmin Brazil domin halartar taro mai taken "Musulunci Addinin Rayuwa Da Tattaunawa Ne" ya isa zuwa wannan kasa, a gefen wannan tafiya, inda ya samu ziyarar masallacin Sayyidina Ali Abi Talib (AS) da ke birnin Curitiba na kasar Brazil, kuma ya yi jawabi ga gungun musulmi a wannan masallaci.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Ziyarar Da Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya Ya Kai Ginin Al'adu Na Masallacin Sayyidina Muhammad Rasulullah (AS) Da Ke Birnin Sao Paulo Kasar Brazil.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (A.S) wanda ya samu gayyata daga musulmin Brazil domin halartar taro mai taken "Musulunci Addinin Rayuwa Da Tattaunawa Ne" ya isa zuwa wannan kasa, a gefen wannan tafiya, inda ya ziyarci sassa daban-daban na gine-ginen al'adun masallacin Sayyidina Muhammad Rasulullah (SAW) da ke birnin Sao Paulo na kasar Brazil.
-
Rahoto Cikin Hatuna Na Halartar Babban Sakataren Majalisar Ahlul-Bait (AS) Ta Duniya A Sallar Juma'a Ta Mabiya Shi'a A Birnin Sao Paulo Na Kasar Brazil 2
Kamfanin dillancin labaran na kasa da kasa na Ahlul-Bait (A.S) ya kawo maku rahoton cewa: Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (A.S) wanda ya samu gayyata daga musulmin Brazil domin halartar taro mai taken "Musulunci Addinin Rayuwa Da Tattaunawa Ne" ya isa zuwa wannan kasa, a gefen wannan tafiya, ya halarci Sallar Juma'ar da 'yan Shi'a ke gabatarwa a Masallacin Manzon Allah SAW da ke birnin Sao Paulo na kasar Brazil.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Ganawar Babban Limamin Cocin Curitiba Na Kasar Brazil Tare Da Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: “Jose Antonio Protzo”, babban limamin birnin Curitiba na kasar Brazil, ya gana da Ayatullah “Riza Ramazani”, Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya Ayatullah Ramadani wanda yayi tafiya zuwa wannan kasa bayan samun gayyata daga Musulman Brazil don halartar taron kasa da kasa mai taken “Musulunci; Addini Ne Na Tattaunawa Da Rayuwa".
-
Rahoto Cikin Hatuna Na Halartar Babban Sakataren Majalisar Ahlul-Bait (AS) Ta Duniya A Sallar Juma'a Ta Mabiya Shi'a A Birnin Sao Paulo Na Kasar Brazil.
Kamfanin dillancin labaran na kasa da kasa na Ahlul-Bait (A.S) ya kawo maku rahoton cewa: Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (A.S) wanda ya samu gayyata daga musulmin Brazil domin halartar taro mai taken "Musulunci Addinin Rayuwa Da Tattaunawa Ne" ya isa zuwa wannan kasa, a gefen wannan tafiya, ya halarci Sallar Juma'ar da 'yan Shi'a ke gabatarwa a Masallacin Manzon Allah SAW da ke birnin Sao Paulo na kasar Brazil.
-
A Ci Gaba Da Tunawa Da Shahadar Imam Sadik (AS);
Rahoto Cikin Hatuna Na Zaman Makoki Shahadar Imam Ja’afarus Sadiq As A Haramin Imamain Kazimain (AS).
Kamfanin dillancin labaran na kasa da kasa na Ahlul-Bait (A.S) ya kawo maku rahoton cewa: a cig aba da tarukan makokin juyayin Shahadar Ima Sadiq As haramin Imamain Kazimain (A.S) ya dauki haramar juyayin shahadar jagoran mazhabar Jafari (A.S) ta hanyar sanya rubuce-rubucen juyayi da bakaken banoni da sitarori.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Halartar Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya A Husseiniyar Muhammad Rasulullah (SAW) Sao Paulo Brazil.
Kamfanin dillancin labaran na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa: Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlul-Bait (A.S) Ta Duniya wanda ya samu gayyata daga musulmin kasar Brazil don halartar taron kasa da kasa mai taken “Musulunci Addini Ne Na Tattaunawa Da Rayuwa" inda ya halarci taron musulmin Brazil a Husseiniyar Muhammad Rasulullah (SAW) a birnin Sao Paulo.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Ganawar Jagora Imam Khamenei Da Gungun Malamai
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci Imam Khamenei- Dz - ya gana da gungun dubban malamai a ranar malamai ta duniya a Husainiyar Imam Khumaini - Allah Ya jikansa - a safiyar yau Laraba 05/01/ 2024.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Halartar Ayatullah Reza Ramezani Wajen Taron Matan Musulmi Na Latin Amurka.
Kamfanin dillancin labaran na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa: Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlul-Bait (A.S) Ta Duniya wanda ya samu gayyata daga musulmin kasar Brazil don halartar taron kasa da kasa mai taken “Musulunci Addini Ne Na Tattaunawa Da Rayuwa" inda ya halarci taron gungun mata musulmin Latin Amurka a birnin Sao Paulo na Brazil tare da gabatar da jawabi.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Gefen Taron " Mai Taken "Musulunci Addini Ne Ta Tattaunawa Da Rayuwa" A Sao Paulo, Brazil
An gudanar da taron kasa da kasa na Musulunci Addini Ne Ta Tattaunawa Da Rayuwa" a birnin Sao Paulo na kasar Brazil, tare da halartar Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (AS). A cikin wannan taron, wakilin ma'aikatar shari'a ta Brazil, wakilin kungiyar Cardinals na kasar, wasu limamai da mabiya addinin kirista na Sao Paulo, jami'an siyasa na Sao Paulo da gungun malamai da masu ruwa da tsaki na kasar da masu tabligi masu addini na Kudancin Amirka ne suka halarta.
-
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA - ya kawo maku rahoton cewa
Rahoto Cikin Hotuna Na Taron Kasa Da Kasa Mai Taken "Musulunci Addini Ne Ta Tattaunawa Da Rayuwa" A Sao Paulo, Brazil
An gudanar da taron kasa da kasa na Musulunci Addini Ne Ta Tattaunawa Da Rayuwa" a birnin Sao Paulo na kasar Brazil, tare da halartar Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (AS).wakilin ma'aikatar shari'a ta Brazil, wakilin kungiyar Cardinals na wannan kasa, wasu limamai da mabiya addinin kirista na Sao Paulo, jami'an siyasa na birnin da jihar Sao Paulo da malamai da kuma masu ruwa da tsaki da masu tabligi masu addini na Kudancin Amirka sun halarta.
-
Ayatullah Ramezani Ya Jaddada Hakan Ne A Ganawar Da Ya Yi Da Ministan Harkokin Wajen Venezuela
A Halin Yanzu Yanayin Gwagwarmaya Ya Bazu A Faɗin Yankin Da Duniya Gaba Daya
Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya bayyana cewa: Guguwar gwagwarmaya ta wuce iyakokin kasar Iran ta kara karfi da fadada zuwa shiyya-shiyya da kuma duniya baki daya ta kuma mamaye zukatan al'ummar duniya duk kuwa da nuna ƙin hakan daga gwamnatoci ma'abuta girman ka.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Ganawar Ayatullah Ramezani Da Shugaban Ƙasar Venezuela
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya maku cikakkun hatunan ganawar Ayatullah Reza Ramezani, Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya a ganawarsa da shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro a ziyarar da ya kai kasar Venezuela.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Ganawar Kwamandojin Sojojin Iran Da Jagora Ayatullah Sayyid Ali Khamenei (Dz)
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: A yammacin yau Lahadi ne tawagar kwamandojin sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gana da babban kwamandan sojojin kasar Ayatullah Khamenei.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Taron Ilimi Mai Taken "Matsayin Makabartar Baqi Da Kuma Bincike Kan Tunanin Wahabiyawa Wajen Rusa Hubbaren Imaman Baqi (A.S)".
Kamfanin dillancin labaran na kasa da kasa na Ahlul-Bait (A.S) ya kawo maku rahoton cewa: A jiya Talata 16 ga watan Afrilu 2024 ne aka gudanar da taron ilimi mai "Matsayin Makabartar Baqi Da Kuma Bincike Kan Tunanin Wahabiyawa Wajen Rusa Hubbaren Imaman Baqi (A.S)" a dakin taro na kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti (AS) _ ABNA_na kasa da kasa. Hoto: Muhammad Husain Khushbaadi
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Sallar Eidul-Fitr A Birnin Alishashr Bushehr Iran
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: An gudanar da gagarumin taron Sallar Eid al-Fitr a birnin Alishahr karkashin jagorancin Hujjatul-Islam Wal-Muslimin Hamidinejad limamin Juma’a na Alishahr, an gudanar da sallar ne a farfajiyar Gulzar Shuhada’i Gumnam da ke Alishahr, 10/04/2024.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Sallar Eidul-Fitr Na 'Yan Shi'ar Amurka A Jihar Michigan
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: an gudanar da sallar idi karama a cibiyar muslunci ta Amurka da ke birnin "Dearborn" a jihar "Michigan" da ke kasar Amurka inda da yawan mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S.) suka halarta.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Sallar Eidul-Fitr A Kauyen Karzakan, Bahrain
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: an gudanar da sallar idi karama a kauyen "Karzkan" da ke kasar Bahrain tare da halartar 'yan shi'a mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) na Bahrain.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Sallar Eidul-Fitr A Cibiyar Musulunci Ta Hamburg
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: an gudanar da sallar Idin karamar Sallah tare da halartar gungun mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) a cibiyar Islama ta Hamburg, daya daga cikin dadaddun cibiyoyi na Musulunci na Shi'a a Jamus.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Sallar Eidul-Fitr A Birnin Kargil Na Indiya
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: An gudanar da sallar Idin karamar sallah a cibiyar tunawa da Imam Khumaini (RA) tare da halartar dimbin mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) da ke birnin Kargil a yankin Kashmir da ke yankin Indiya.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Sallar Eid Al-Fitr Na 'Yan Shi'ar Pakistan A Birnin Lahore
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: an gudanar da sallar idin karamar Sallah a karkashin jagorancin Hujjatul Islam Wal Musulmi ‘Sayyid Jawad Naqwi’ a masallacin ‘Bait al-Atiq’ da ke cikin makarantar hauza ta "Jami’atul Urwatul Wusqa" a birnin Lahore na kasar Pakistan.