-
Hotunan Zaman Juyayin Ashura Rana Ta 4 A Garin Jos
Yau Laraba 10/July/2024 Daidai da 4/Muharram/1446 an Shiga Rana ta 4 da Fara Zaman Juyayin Ashura na Tunawa da Kisan Imam Hussain tare da Iyalansa da Sahabansa a Filin Karbala. Da yake Yau Wakilin Ƴan'uwa Almajiran Shaikh Zakzaky (H) na Garin Jos Shaikh Adamu Tsoho baida Lafiya shine Malam Abubakar Sulaiman ya Gabatar da Jawabi a Madadin su Shaikh Adamu Tsoho. Muna Fatan Allah Ya Baiwa Su Shaikh Lafiya Aba Abdullahil Hussain As
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Taron Dinkin Kayan Jarirai Na Husaini A Haramin Mai Tsarki Na Razawi
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya kawo maku rahotan cewa: an dinka tufafi guda 12,000 don gudanar da taron jarirai na Husaini a daidai lokacin da watan Muharram ya kama inda ake gudanar da makokin Sayyidush Shuhada’a (a.s) tare da halartar 'yan'uwa mata masu hidima 800 a cikin ma’akatar dinki haramin Razawi Mai Tsarki.
-
Muhimmancin Kuka Akan Musibar Imam Husaini As
Digon Hawaye Mafi Nauyi ▪️ Digon hawayen da ake zubarwa a lokacin tuna musibar Imam Hussaini (As) shi ne digon hawaye mafi nauyi a duniya. Imam Riza (a.s) ya yi magana da Ɗan Shabib yana mai cewa: Ya dan Shabib, idan ka yi wa Hussaini (A.S) kuka har hawayenka suka gangaro bisa kumatunka, Allah zai gafarta maka duk wani zunubi da ka aikata, karami ko babba, kadan ko dayawa. ▫️ Amali, Sheikh Sadouq, shafi na 192.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Taron Kasa Da Kasa Na Shahidan Kare Haramin Da Gwagwarmaya A Birnin Mashhad - 2
An gudanar da taron jiya asabar 29 ga watan Yuli 2024t a hubbaren Imam Riza (a.s) da ke birnin Mashhad.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Taron Kasa Da Kasa Na Shahidan Kare Haramin Da Gwagwarmaya A Birnin Mashhad - 1
Rahoto Cikin Hotuna Na Taron Kasa Da Kasa Na Shahidan Kare Haramin Da Gwagwarmaya A Birnin Mashhad - 1
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Maulidin Imam Hadi (A.S) A Haramin Imam Ridha As Mashhad Razawi
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya habarta cewa, an gudanar da maulidin Imam Hadi (a.s) na musamman ga wadanda ba Iraniyawa ba tare da jawabin "Hujjatul-Islam Wal-Muslimin "Syed Mohammad Safi" "a cikin farfajiyar Ghadir na haramin Razawi mai tsarki. A gefen wannan shirin, Abdul Reza Husain Al Saigh daga Kuwait ya zana zane mai taken "Aliya Man Ali".
-
Rahoto Cikin Hotuna Na: Taro Mai Taken "Bunkasasshen Zaɓe; Karfin Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Take Da Shi A Fagen Kasa Da Kasa" A Birnin Qum
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (a.s) - ABNA - ya kawo maku rahoto cikin hotuna na taron da aka gabatar mai taken "Bunkasasshen Zaɓe; Karfin Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Take Da Shi A Fagen Kasa Da Kasa" a zauren majalisar Ahlul-Baiti As ta duniya, a birnin Qum. Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar ne ya gabatar da jawabi a wannan taro, wanda ya samu halartar gungun 'yan kungiyar "Shahid Arman Media Center". Hoto: Hamid Abedi
-
Labarai Cikin Hotuna / Magoya Bayan Falasdinu Sun Zagaye Fadar White House Amurka
Ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar adawa da kisan gillar da Isra'ila ke yi wa mutanen Gaza a duk fadin duniya. Dangane da haka, masu zanga-zangar da suka taru a Washington, babban birnin kasar Amurka, domin nuna goyon baya ga Gaza, sun kafa tantuna a gaban fadar White House tare da sanar da cewa za su ci gaba da zanga-zangar ruwan sanyi da suke gabatarwa.
-
An Raba Arziki Ga Kowa Kuma Ajalin Kowa Tabbatacce Ne!
An raba Arziki kuma ajali tabbatacce ne! Imam Husaini (a.s): Kamewa ba ta hana Arziki, kuma kwaɗayi ba ya kawo daukaka, domin shi arziki a rabe ya ke kuma Ajali tabbas ne, kuma yin kwaɗayi zunubi ne.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Jawabin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Wajen Taron Cika Shekaru 35 Da Wafatin Imam Khumaini (RA).
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (A.S) ya habarta cewa, A safiyar yau ne aka gudanar da taron tunawa da 35 da wafatain Imam Khumaini Qd wanda ya assasa jamhuriyar musulunci ta Iran wanda Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya halarta tare da gabatar da jawabi ga masoyan wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Taron Girmama Shahidan Hidima Wanda Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya Da Jami'atu Al-Mustafa Suka Gabatar (2).
Manyan malamai wadanda suka gabatar da jawabi a wannan taron sun hada da Ayatullah Ramazani, babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (a.s) ta duniya da Hujjatul Islam Wal Muslimeen, Dr. Abbasi, shugaban Jama'atul-Mustafa da Hujjatul-Islam Wal Muslimeen, Abdallah Al Daqqaq, shugaban makarantar hauza na Bahrain
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Taron Girmama Shahidan Hidima Wanda Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya Da Jami'atu Al-Mustafa Suka Gabatar (1).
An gudanar da taron tunawa da shahidan hidima da majalisar Ahlul-baiti (A.S) da jami'ar Al-Mustafa Al-Alamiya a dakin taro na Quds na Masallacin Imam Khumaini (RA) dake birnin Qum. Malamai wadanda suka gabatar da jawabi a wannan taron sun hada da Ayatullah Ramazani, babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (a.s) ta duniya da Hujjatul Islam Wal Muslimeen, Dr. Abbasi, shugaban Jama'atul-Mustafa da Hujjatul-Islam Wal Muslimeen, Abdallah Al Daqqaq, shugaban makarantar hauza na Bahrain. Hoto: Hamid Abed
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Taron Juyayin Shahidan Hidima A Hubbaren Karimatu Ahlul-Baiti (a.s) Qum.
Kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait - ABNA ya bayar da rahoton cewa: an gudanar da taron juyayin shahadar shahidan hidima tare da jawabin Hujjatul-Islam Walmuslimeen Sayyid Muhammad Saeedi da waken jaje daga bakin Abbas Haidarzadeh da halartar shugabannin Iran da jami'an soji na lardin Qum, wanda sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka shirya a hubbaren Sayyidah Ma'asumah Karimatu Ahlul Baiti (a.s) a birnin Qum.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Taron Juyayin Shahidar Ayatullah Raisi A Masallacin Arak Na Birnin Tehran
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (A.S) ABNA ya kawo maku rahotan cewa: an gudanar da taron juyayin shahadar shugaban kasar Iran Ayatullah Sayyid Ibrahim Raisi da abokan shahadarsa a masallacin Arak da ke birnin Tehran.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Ganawar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Da Iyalan Shahidai Masu Daraja.
Labarai Cikin Hotuna Na Ganawar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Da Iyalan Shahidai Masu Daraja.
-
Dakarun Hizbullah 313 Su Kai Shahada Tun Bayan Kai Garin Guguwar Al-Aqsa
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: An kiyasta adadin shahidan kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon tun bayan lokacin hare-haren da guguwar Al-Aqsa da cewa sun kai mutane 313.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Yadda Ake Gudanar Da Rakiyar Jana'izar Shahidan Hidima A Birnin Mashhad
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: tare da halartar miliyoyin al'ummar a birnin Mashhad ana ci gaba da gudanar taron rakiya da Juyayin Shahadar Shugaban Kasar Iran Da Abokan Tafiyarsa cikin tari na musamman mai cike da dinbin al'ummar duniya. Hoto: Muhsin Rahimi Anbaran
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Yadda Aka Gudanar Da Rakiyar Gawar Shahidan Hidima Na Iran A Birnin Tehran
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa:, an gudanar da rakiyar gawar shahid Ayatullah Sayyid Ibrahim Raisi shugaban jamhuriyar musulunci ta Iran da sauran shahidan hidima tare da halartar miliyoyin jama'a daban-daban daga jami'ar Tehran zuwa Maidan Azadi na wannan birni. Hoto: Hamid Abedi
-
Alkur'ani: Kada Ku Ce Wa Wadanda Suka Aka Kashe A Kan Tafarkin Allah Matattu Ne...
وَلَا تَقُولُوا لِمَنْ يُقْتَلُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ أَمْوَاتٌ ۚ بَلْ أَحْيَاءٌ وَلَٰكِنْ لَا تَشْعُرُونَ Kuma kada ku ce: " ga wanda aka kashe a kan tafarkin Allah matattu ne, ba haka ba ne lalle su rayayyu ne sai ku amma bakwa riskar hakan." Do not call those who were slain in Allah’s way ‘dead.’ No, they are living, but you are not aware
-
Annabi Muhammad Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A Gare Shi: Saman Ko Wane Aikin Alkhairi Akwai Wani Aikin Banda Mutuwa A Tafarkin Allah...
Annabi Muhammad Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A Gare Shi: "فَوْقَ كُلِّ ذى بِرٍّ بِرٌّ حَتّى يُقْتَلَ الرَّجُلُ فى سَبيلِ اللّه ِ فَلَيْسَ فَوقَهُ بِرٌّ". "Sama da kowane aikin alheri, akwai wani aikin alheri, har sai an kashe mutum a tafarkin Allah, domin babu wani aiki na alheri sama da shi". Bihar Anwar, juzu'i na 74, shafi na 60, h 25.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Makokin Shahidan Hidima Na Iran A Birnin Tabriz 2
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: an gudanar da raka gawarwakin shahidai: Ayatullah Raisi da sahabbansa a birnin Tabriz tare da halartar dimbin al'ummar kasar daga sassa daban daban na kasar a kan titunan dandamalolin birni Tabriz. Hoto: Masoud Sepehrinia
-
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Masoyi Raisi Bai San Gajiyawa Ba
An Buga Rubutun Hannun Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Na Girmama Shahidi Shugaban Kasar Iran Sayyid Ibrahim Raees: Raisi Azez Bai San Gajiyawa Ba.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Makokin Shahidan Hidima Na Iran A Birnin Tabriz
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: an gudanar da raka gawarwakin shahidai: Ayatullah Raisi da sahabbansa a birnin Tabriz tare da halartar dimbin al'ummar kasar daga sassa daban daban na kasar. Hoto: Masoud Sepehrinia
-
An Ɗora Tutar Makoki A Kan Ƙubbar Haramin Imam Ridha As
An Ɗora Tutar Makoki A Kan Ƙubbar Haramin Imam Ridha As Domin jajantawa shahadar Khadimul-Ridha, Shahidai Ayatullah Sayyid Ibrahim Raisi
-
Sayyid Majid: Idan Na Yi Shahada Ku Yaɗa Wannan Hoton Nawa + Bidiyo
Behzad Parvinqods (mai daukar hotounan yaki) daga gareshi aka nakalto wannan bidiyo: Ku yi addu'ar Allah ya sa mutuwata ta zama shahada a tafarkin Allah Madaukakin Sarki... Sayyid Majid Al Hashim Na Azarbaijan Ya Samu Cikar Burinsa...
-
Hoton Farko Na Tarkacen Jirgin Saman Da Ke Ɗauke Da Shugaban Kasar Iran
Wanda Ke Nuna Akwai Yiyuwar Shahadar Shugaban Ƙasar Da Dukkan Abokan Tafiyarsa. Masu Ceto Sun Isa Wurin Da Ke Kusa Da Tarkacen Sauran Helikwaftan Za a sanar da tabbataccen labari game da makomar jirgin da ya fado a hukumance nan da 'yan wasu lokuta. A cewar Kolivand, shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent, abin takaici, labari mai dadi bai iso ga kunnuwa ba.
-
Bidiyo Da Hotunan Farko Na Wurin Da Jirgin Da Ke Ɗauke Da Shugaban Ƙasar Iran Ya Faɗi
Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti - Abna: Bidiyo da Hotunan farko na jirage quadcopter da ke bincike wajen gano inda jirgin da ke dauke da shugaban kasar Iran ya yi hatsari.
-
An Gudanar Da Taron Yaye Mahaddata Alkur'ani Karo Na 13 A Birnin Kano + Hotuna
Anyi wannan gagarumin taro ne, a yau Asabar 10/11/1445 AH, 18/05/2024 AM. Wanda ya gudana a Farfajiyar Filin Babban Masallacin Jumu'a na Jahar na kofar gidan Sarkin Kano, Alh Aminu Ado bayero.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Biki Na Musamman Na 'Yan Mata Na Ƙasa Da Ƙasa A Yayin Bukin Kwana Goma Na Karama A Qom
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: an gudanar da wani biki na musamman ga 'yan mata na kasa da kasa na zagayowar kwanaki goma na karama tare da gabatar da shirye-shirye daban-daban da suka hada da laccoci na ilimantarwa, wakokin yabo, karatuttukan wakokin gasa a cikin haramin hubbaren Sayyidah Ma'asumah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Ƙawata Haramin Imam Husaini Da Imamain Askarain As Da Banonin Imam Ridha As
Kamfanin Dillancin Labaran shafin Sadarwa Na Ahlul Bayt (AS) Na - ABNA - Ya Habarta Maku Cewa: Bisa Ga Munsabar Zagayowar Haihuwar Imam Ridha As An Sanya Banoni Masu Ɗauke Da Rubuce-Rubuce Na Ado Da Sunan Imam Ridha (a.s) A Cikin Haramin Imam Husaini da Imamain Askarain (Amincin Allah Ya Kara Tabbata A Gare Su).