-
Hizbullah Ta Tayi Ruwan Rokoki A Yankin Golan | Yahudawa Sun Martani Ga Ministan Tsaro Da Cewa: Barka Da Safiya! + Bidiyo.
Hizbullah Takai Harin Makami Mai Linzami Da Jiragen Sama Maras Matuki Kan Arewacin Falasdinu Da Aka Mamaye Da Yankin Golan Na Kasar Syria + Bidiyo.
Jaridar yahudawan sahyoniya ta Yediot Aharnot ta bayyana hare-haren na yau da kungiyar Hizbullah ta kai a kasar Labanon a matsayin mai hadari da ba a taba ganin irinsa ba.
-
Bidiyon Yadda Wasu Iyaye Mat Masu Shekaru Sama Da 60 Ke Gudanar Da Tattakin Arbaeen Husain As
Wadannan matan sun dauki kusan kwanansu shida kenan suna tafiyar tattakin yayin tattaunawa da daya daga cikinsu tace suna gudanar da tattakin cikin koshin laafiya amma da sun kasance a gida ne da suna cen jikinsu na tai masu ciwo amma albarkar soyayyarsu da Imam Husain As ya zamo agshi suna iya tafiya na wanna tattakin.
-
Rahoton Taron Tunawa Da Ranar 'Yan Jarida A Kamfanin Dillancin Labarai Na Ahlul-Baiti (AS) - Abna + Hotuna Da Bidiyo
An gudanar da taron shekara-shekara na abokan aikin kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA – tare da halartar Ayatullah "Ramazani", babban sakataren majalisar Ahlul-Baiti (AS) ta Duniya.
-
Game da wannan, an gabatar da bidiyon mai taken "Wannan Tafarkin Zai Ci Gaba Har Zuwa Bayyanar Mai Ceto..." ga masu sauraron.
Bidiyo| Wannan Tafarkin Zai Ci Gaba Har Zuwa Bayyanar Mai Ceto ...
Gwamnatin sahyoniyawan da abar kyama ta sake kara wani tarihin cin zarafin bil'adama ta hanyar kashe shahidi Ismail Haniyyah, shugaban siyasar Hamas. Wannan ta'addanci a fili yake ga dokokin kasa da kasa, laifi ne da ba za a yafe ba, tare kuma da keta Kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a bainar jama'a. Shahid Ismail Haniyah ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da Falasdinu da kuma dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Falasdinu.
-
Bidiyon Yadda Akai Jana'izar Matar Da Ta Yi Shahada A Harin Da Gwamnatin Sahayoniya A Kudancin Kasar Labanon.
Bidiyon Yadda Akai jana'izar matar da ta yi shahada a harin da gwamnatin Sahayoniya ta kai a unguwar Beirut da ke kudancin kasar Labanon.
-
Isra'ila Ba Zata Cika Shekaru 80 Ba Za'a Shareta
Tsohuwar hirar da aka yi da shahidi Sheikh Ahmad Yasin wanda ya kafa kungiyar Hamas, game da makomar da kuma ruguza gwamnatin sahyoniyawa. Acikin wannan tattaunawa ya fada cewa za a halaka Isra'ila a 2027 Wannan alkawari ne na Allah. Insha Allahu Naftali Bint, tsohuwar Firayi Ministan Isra’ila, ta sha fadin cewa Isra’ila ba za ta cika shekaru 80 a duniya ba a shekarar 2027.
-
Bidiyo Ɗaukar Sama Na Yadda Aka Gudanar Da Jana'izar Shahid Isma'il Haniya A Tehran
Abin sha'awa Halartar Al'ummar Iran A Cikin Yanayin Zafi A Don Jana'izar Babban Baƙon su
-
Sabon Bidiyo Na Kwamandan Kungiyar Hizbullah Da Ya Yi Shahada A Kasar Labanon + Hoto
Cibiyar yada labaran yakin Hizbullah ta kasar Labanon ta watsa bidiyon jawabin shahid kwamanda Fu’ad Shukri a cikin gungunr mayakan Hizbullah.
-
Hizbullah Ta Sake Jefa Rayuwar Sahyoniyawa Cikin Tsoro Da Fargaba Bayan Ta Aike Da Tsuntsun Hudhuda 3 Domin Liken Asiri Zuwa Wuraren Tsaron Isra’ilawa
Sabbin ayyukan Hizbullah na "Hudhud 3" a sararin samaniyar yankunan da aka mamaye + bidiyo a sabon kutsen da ya yi a sararin samaniyar yankunan da aka mamaye, Hudhud 3 ya dauki hotuna daga sansanin tsaron sama na yahudawa a karon farko.
-
Yadda Tattakin Juyayin Shahadar Imam Husaini As Na Malaman Makarantun Shi'a A Tanzaniya Ya Gudana + Hotuna Da Bidiyo
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: a ranar sha hudu ga watan Muharram ne aka gudanar da jerin gwano na juyayin shahadar Imam Husaini As wanda malamai da daliban makarantun shi'a na kasar Tanzania suka gabatar domin yin juyayin shahadar Sayyidina Aba Abdullah Husain (A.S) da kuma goyon bayan yaran Gaza.
-
Bidiyo Cikakkun Bayanai Na Harin Da Gwamnatin Yahudawa 'Yan Mamaya Ta Kai A Yaman
Yamen Zata Mayar Da Martani: Tashar Jiragen Ruwan Haifa Da Aka Mamaye Ita Ce Hadafin Da Yamen Za Ta Kai Wa Hari.
-
Isra'ila Ta Kai Hari Tashar Jiragen Ruwa Ta Hudaida Yaman + Bidiyo
Al-Mayadeen: Sojojin yahudawan sahyoniya sun kai hari kan birnin Hudaidad da jiragen yakinta na F-35.
-
Labarai Cikin Bidiyo: Yadda Makokin Baki Asad Ya Gudana A Karbala Na Tunawa Da Ranar Da Aka Binne Shahidan Karbala
Bidiyo Daga Karbala Ma'alla na gudanar da taron makokin Bani Asad na zagayowar ranar da aka binne shahidan Karbala.
-
Yadda Aka Muzahara Ranar Ashura A Jihar Michigan Ta Amurka + Bidiyo
Yadda Makokin Al’iummar jihar Michigan ta Amurka ya gudana tare da daga tutar Falasdinu Muzahara ranar Ashura a jihar Michigan ta Amurka tare da amsa kran Labbaika Ya Husain, Labbaika Ya Khamenei tara da tunawa da shahidan Karbala da na Gaza. Idan bamu a Gaza, a kalla ya kamata mu zama muryarsu ga al'ummar duniya, mu yada a kafofin yada labara irin zaluncin da akewa al'ummar Palastinu. Kamar kowace shekara, an gudanar da tarukan Tasu'a da Ashurar Imam Husaini tare da hadin guiwar kungiyoyin makoki a birnin "Dearborn" dake jihar Michigan ta kasar Amurka. Masu zaman makoki - wadanda kasantuwar mafi yawansu samari ne ya burge sosai - sun sabunta alkawarinsu da Sayyidushl-Shuhada (a.s) da sunnonin Ashurai da anbaton "Labbaik Ya Husain". Wani abin ban sha'awa sosai a taron makoki na jihar Michigan a wannan shekara shi ne daga tutar Falasdinu don nuna goyon baya ga al'ummar Gaza da kuma tutoci na yin Allah wadai da laifuffukan gwamnatin sahyoniyawan da ke kashe kananan yara. Har ila yau, sun daga zane-zane da hotuna a hannunsu wadanda suka kwatanta laifin ta’addanci da Yazid ya aikata a shekara ta 61 bayan hijira da kuma laifukan da Isra'ila take aikata a duniya a yau ga mutanen Gaza da Falasdinu. Masu makoki na Husain a Michigan sun kuma yi kira ga Musulmi da masu ‘yanci na duniya da su kaurace wa kayayyakin Isra’ila.
-
Gwamnatin Yahudawa Ta Jefa Bama-Bamai 8 A Kan Gazza A Kokarinta Kashe Muhammad Daif
Tan 8 na bama-bamai ne gwamnatin sahyoniyawan ta jefa a Gaza a yunkurinta na karshe na kashe Muhammad Al-Daif
-
Muhammad Jabara Daya Daga Cikin Jagororin Kungiyar Jama'atu Islami Ya Yi Shahada + Bidiyo
Muhammad Jabara Daya Daga Cikin Jagororin Kungiyar Jama'atu Islami Ta Kasar Labanon Ya Yi Shahada bayan da yahudawan sahyuniya suka kai wa motarsa hari a yammacin Bekaa na kasar Labanon.
-
Iran: Da Dumimi / Dr. Mas’ud Pezeshkian Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Iran + Bidiyo
Dr. Mas’ud Pezeshkian yaa lashe zaben shugaban kasar Iran bisa dogaro da Jimlar kuri'u da aka kirga: 30,530,157 wanda ma’aikatar zaben kasar ta fitar.
-
Ansarullah Ta Kaddamar Da Karamin Jirgin Ruwanta Mai Taken "Tufanul-Madammar" + Bidiyo
Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta kaddamar da karamin jirgin ruwan kai harinta mai taken "Tufanul-Madammar" (Ambaliya Mai Barna).
-
Bidiyon Yadda Miliyoyin Al'ummar Iran Suka Fito Domin Jefa Kuri'arsu A Akwatinan Zaben Shugaban Ƙasar Karo Na 14.
Al'ummar sun fito kwansu da kwarkawatarsu wajen yin sahun domin gudanar da zaɓen shugaban kasar karo na 14.
-
Bidiyon Yadda Ake Ci Gaba Da Kaɗa Ƙuri'u A Birnin Mashhad Iran A Haramin Imam Ridha As
Bidiyon Yadda Maziyarta Haramin Razawi Suke Taka Rawar Gani A Zaɓen Shugaban Ƙasa Karo Na 14. A yau farfajiyar haramin Imam Riza (a.s) da sararin fadin haramin Imam Rida (a.s) ya zamo wajen r zaɓe inda dinbin al'ummar birnin Mashhad da kewaye dama wadanda suka zo ziyara ke kada kuri'arsu a cikinsa.
-
Hizbullah Ta Gargadi Sahyoniyawa: Tabbas Za Ku Yi Nadama + Bidiyo
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Labanon ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna muhimman wurare da cibiyoyi da ke cikin Palastinu da Isra’ila ta mamaye tare da gargadin 'yan mamaya da cewa za su yi nadama idan aka samu kazamin fada.
-
Bidiyo | Haramin Imam Husaini Ya Karbi Bakuncin Takwaransa Na Alawiyyah Dauke Da Tutar Imam Ali (A.S).
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlal-Bait (AS) -ABNA- ya habarta cewa: haramin Imam Husaini mai alfarma ya karbi bakuncin wata tawaga daga haramin Alawiyya mai alfarma dauke da tutar Imam Ali (a.s). inda ka shiga da wanna tutar cikin haramin Imam Husain As wanda za’ai bukin dora tutar a haramin Ima Husain As a ranar Juma’a.
-
Bidiyo Ganawar Baqiri Da Ismail Haniyah
Bidiyo Ganawar Baqiri Da Ismail Haniyah
-
Bidiyoyi | Na Sabbin Ikrarin Da Mambobin Kungiyar Leken Asirin Amurka Da Isra'ila Da Ke Yemen Suka Yi
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti - ABNA ya bayar da rahoton cewa: a yammacin jiya ne hukumar tsaron kasar ta fitar da wasu sabbin ikirari da wasu gungun 'yan kungiyar leken asiri na Amurka da Isra'ila suka yi wannan sanarwar ta fito ne daga jami'an tsaron kasar bayan kama wadannan jami’an asiri.
-
Karin Wasu Bidiyoyin Na Kisan Kiyashin Da Sahayoniya Su Kai A Sansanin Nusairat
Gwamnatin yahudawan sahyuniya sun rusa tsakiyar Gaza da bama-bama, ta hanyar da gwamman jiragen yakin Isra'ila da jirage masu saukar ungulu su yi ruwan bama-bamai a tsakiyar zirin Gaza. Ya zuwa yanzu dai mutane 150 ne suka yi shahada, wasu da dama kuma sun samu munanan raunuka, kuma wadanda ba a san adadinsu ba suna karkashin baraguzan ginin.
-
Bidiyo | Na Yanayin Farko Na Harin Bama-Bamai A Nusairat A Tsakiyar Zirin Gaza Tare Da Daruruwan Shahidai Da Jikkatar Wasu.
Bidiyo | Na Yanayin Farko Na Harin Bama-Bamai A Nusairat A Tsakiyar Zirin Gaza Tare Da Daruruwan Shahidai Da Jikkatar Wasu.
-
Ci Gaba Tattaunawar Shekh Zakzkay (H) Da Wakilan Kamfanin Labarai Na ABNA
Shekh Zakzaky: Sakona Zuwa Ga Dukkan Musulmi Shi Ne Su Manta Da Sabanin Da Ke Tsakaninsu, Su Sani Cewa Suna Da Lamari Kwara Guda Ne Dubi Halin Da Ake Ciki A Gaza
Manzon Allah (S.A.W) ya ce a cikin ruwaya cewa Musulmi kamar jiki guda ne cewa idan wani bangare ya yi ciwo to sauran sassan ma za su yi ciwo. Sai dai kash, mu musulmi mun rabu, kuma ya zama dole mu manta da batun bangaranci, mu tuna cewa mu al’umma daya ce, masu lamari daya. A daya bangaren kuma, muna ganin makiya duk da ra'ayoyi mabanbanta da suke da, amma sun tsaya kan layi daya, sun hada kai don fuskantar musulmai.
-
Bidiyoyin Yadda Yahudawan Sahyuniyawa Suka Shiga Masallacin Al-Aqsa Don Gudanar Da Ibadar Talmud A Safiyar Yau
Tun da sanyin safiya zuwa yau ne sama da 'yan sahayoniya 500 'yan mamaya ne suka kai dafifin shiga masallacin Al-Aqsa karkashin taimakon jami'an 'yan sanda tare da gudanar da ayyukan ibada na Talmud. A halin da ake ciki dai wasu da dama daga cikin yahudawan sahyuniya sun yi ta rawa, da tattakawa, da kuma rera wakoki na tsokana, kafin su danna cikin masallacin Al-Aqsa da ke tsohon yankin Kudus. Wanda Sahayoniyawan sun yi wannan shirin ne don tsokana a birnin Quds a yau.
-
Yanzu-Yanzu: Bidiyoyin Harin Ta’addancin Kare Dangi Na Kisan Kiyashin Da Isra’ala Ta Ke Aikatawa A Yau Din Nan
Wadannan laifuka na ta’addanci ba su da iyaka gwamnatin 'yan ta'addar yahudawan sahyoniya na ci gaba da kashe fararen hula a Gaza ba kakkautawa mafi yawansu yarana ne kanana.
-
Wasu Yankuna Na Bidiyoyin Jawabin Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin Iran A Taron Tunawa Da Shekaru 35 Da Wafatin Imam Khumaini Qs
Wannan rahoton yana dauke da bidiyoyin da suka hada da lokacin da jagoran juyin juya halin Musulunci ya shiga haramin Imam Khumaini tare da fara gabatar da jawabai na zagayowar ranar cika shekaru 35 da wafatin Imam mai girma jagoran juyin juya halin Musulunci, rahamar Allah a gare shi.