?>

Ziyarar Shugaban Kasar Siriya A Tehran Bude Wani Sabon Shafin Dangantaka Ne

Ziyarar Shugaban Kasar Siriya A Tehran Bude Wani Sabon Shafin Dangantaka Ne

Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Abdollahiyan shi ne ya furta hakan a wata hira da yayi da cibiyar dake yada ayyukan jagoran juyin musulunci na Iran Imam Khamna’I inda ya bayyana cewa Ziyarar da Bashar Asad shugaban kasar Siriya ya kawo nan birnin Tehran ta guna ne a wani yanayi na yan uwantaka da abokantaka kuma samar da wani sauyi a tarihin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban Asad na siriya ya gana da jagoran juyin juyin musulunci na iran da kuma shugaban Ibrahim ra’isi kuma ya isar da sakon cewa dangantakar dake tsakanin kasahen biyu ta dabance kuma ba za ‘a taba rabuwa da juna ba

Abdollahiyan ya kara da cewa alakar kasashen biyu ta dauki wani sabon salo a baya bayan nan domin ta kunshi ci gaban tattalin arziki kasuwanci yawon bude Ido bugu da kari kuma da bangaren ayyukan soji da kuma tsaro.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*