?>

Zarif : Dole Ne Amurka Ta Sake Komawa Ga Yarjejeniyar Nukiliya

Zarif : Dole Ne Amurka Ta Sake Komawa Ga Yarjejeniyar Nukiliya

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya bayyana cewa dole ne Amurka ta sake komawa ga yarjejeniyar nukiliya ta hanyar cire duk takunkumin da aka kakaba wa Iran.

ABNA24 : Mista Zarif, na bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da tashar talabijin ta Press Tv.

Bayyanin na ministan harkokin wajenkasra ta Iran, na zuwa ne a daidai lokacin da AMurka ta bayyana cewa a shirye ta ke ta shiga tattaunawa da Iran, tare da sauren kasashen da suka rage a yarjejeniyar da aka cimma da Iran a shekarar 2015.

kuma a cewar Zarif, Iran, za ta shiga wata tattauanwa ne da sharadin dukkan kasashen dake cikin yarjejeniyar sun cika alkawuran da suka dauka game da yarjejeniyar.

A daya bangaren kuma ya ce sabon shugaban AMurka Joe Biden, babu wani abu da ya yi kan siyasar Iran kamar yadda ya yi alkwari yayin yakin neman zabe, kuma yanzu haka yana ci gaba ne akan siyasar matsin lamba da Donald Trump kan Iran.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni