?>

Zanga-zangar kyamar Amurka a sassa daban-daban na kasar Yemen

Zanga-zangar kyamar Amurka a sassa daban-daban na kasar Yemen

Al'ummar kasar Yemen sun fara gudanar da zanga-zangar nuna kyama ga Amurka a larduna daban-daban na kasar bisa taken "Amurka ce ke bayan yakin soji da na tattalin arziki da ci gaba da yaki da kuma mamaye kasar Yemen."

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- ya habarta cewa, a safiyar yau litinin ne al'ummar yankin Sa'ada da ma wasu larduna da dama suka fara gudanar da zanga-zangar, biyo bayan kiran da kwamitin shirya zanga-zanga a kasar Yemen ya yi na gudanar da zanga-zangar kyamar Amurka a duk fadin kasar ta Yemen.

Mutan Yaman sun gudanar da zanga-zangar tare da ga taken nuna kyama ga Amurka.

Mahalarta zanga-zangar kyamar Amurkawa sun daga tutocin kasar Yemen tare da rike allunan nuna kyamar Amurkawa irinsu "Amurka babbar shaidan ce," suna yin Allah wadai da ta'asar Amurka da rawar da take takawa a yakin Yemen.

Kamfanin dillancin labaran na Abna ya nakalto daga shafin tashar Al-Mayadin cewa, lardunan Taiz, Hajjah, Imran, Al-bayda, Rima da Saada sun fara gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnatin Amurka tun a safiyar yau, mai taken: “Amurka ce ke bayan rikicin soji da tattalin arziki da kuma ci gaba da yakin da kuma mamayar Yemen.

Kwamitin shirya zanga-zangar na kasar Yemen ya kuma yi kira ga al'ummar kasar Yemen da ke sauran sassan kasar da su shiga sahu wajen zanga zangar nuna kyama ga Amurka.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*