?>

Zaman kwana bakwai da Shahadar Shahid Haidar Ali da Shahida Batula a Iran

Zaman kwana bakwai da Shahadar Shahid Haidar Ali da Shahida Batula a Iran

A jiya Litinin 29-7-2019 aka gabatar da addu’a hadi da biki ga waddannan jaruman shahidanmu *(shaheed Hydar Ali)* da *(shaheeda Batula Muhammad Gana)* da aka gabatar a jamhuriyan musulunci ta Iran.

(ABNA24.com) A jiya Litinin 29-7-2019 aka gabatar da addu’a hadi da biki ga waddannan jaruman shahidanmu *(shaheed Hydar Ali)* da *(shaheeda Batula Muhammad Gana)* da aka gabatar a jamhuriyan musulunci ta Iran.

Taron wadda yahada ‘yan kasashen Afrika wadanda suke karatu a birnin Qum da wasu ‘yan asalin kasar Iran.

Alahhamdulilah bayan anyi saukan Alkur’ani maigirma sai aka kira wasu daga cikin dalibai sukayi karatu , sannan aka kira mai jawabi *(Hujjatul islam wal muslimin shaikh Abdullahi zango)*

A lokacin jawabin nasa Shaikh ya tabo tarihin harkan nan sannan da jarabawoyin da harkannan ta fuskanta , sannan har ya kai ga yadda makiya suka matsa da dadin takura wa harkannan, sannan ya tabo zaluncin da akeyi ake kuma ci gaba dayi wa *(Sayyid zakxaky H)*

Sannan ya ci gaba da dorawa kan wadannan jaruman shahidan *shaheed Hydar* da *shaheeda Batula* cewa wadannan bayin Allah sun sami babban rabo wadda ba kowa bane yake samu , daga ciki yake cewa kwata kwata bai wuce kwan 10 da barinsa nan ba yaje ya samu wannan babban rabo wadda Allah ya azurtashi , sannan shaheda BATULA ta kasance mahaddaciyar Alkur’ani mai girma wadda shima wannan baiwa ce sai wanda Allah ya zaba yake baiwa ita.

Alahhamdulilah anyi lafiya anyi addu’a.
/129


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*