?>

Yau Ce Ranar Babbar Sallah A Mafi Akasarin Kasashen Musulmi

Yau Ce Ranar Babbar Sallah A Mafi Akasarin Kasashen Musulmi

A yau ne kasashen musulmai da dama suke gudanar da bukukuwan babbar sallah, ko kuma sallar layya, daya daga cikin bukukuwa na shekara-shekara mafi muhimmanci a addinin musulinci.

ABNA24 : Bayan kammala sallar idin dai musulmai masu hali kan yanka dabbobin layya a wani nau'i na ibada.

Wannan dai shi ne karo na biyu a jere da musulmai ke gudanar da bukukuwan babbar sallah cikin yanayi na fama da annobar korona data addabi duniya, wanda ya sanya kasashe da dama suka takaita yanayin yadda aka saba gudanar sallar a shekarun baya.

Sallah'r layya dai na zuwa ne kwana daya bayan masu aikin hajji sun yin hawan dutsen Arafat, a ci gaba da aikace aikacen hajji, wanda a bana shi ma ya takaita ga mazauna Saudiyya 60,000 kawai.

Hukumomin Saudiyya dai sun takaita yawan masu aikin hajji saboda fargabar yaduwar sabbin nau’ukan cutar korona.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*