?>

Wata Tawagar Iran Ta Isa Iraki Domin Binciken Kisan Janar Qasem Soleimani

Wata Tawagar Iran Ta Isa Iraki Domin Binciken Kisan Janar Qasem Soleimani

Wata tawagar masu bincike kan sha’anin shari’a ta Iran, ta isa Iraki domin gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yi wa Janar Qasem Soleimani a watan Janairun 2020.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Bayan isa Baghdad, tawagar alkalan Iran ta samu tarba daga shugaban majalisar koli ta shari'a ta Iraki Faiq Zidan.

A ranar 3 ga Janairun 2020, ne Janar Qassem Sulaimani da Abu Mahdi Almuhanddis da wasu dake tare da su sukayi shahada a kusa da filin jirgin saman Baghdad, a wani harin jirgi marar matuki da Amurka bisa umarnin tsohon shugaban kasar Donald Trump, ta kai.

Har yanzu Iran ba ta huce takaicin kisan janar din na ta ba, mutumin dake da babbar kima a kasar.

Bayan kisan gillar, dakarun kare kare juyin juya halin musulinci na Iran, IRGC sun kai wani farmaki kan sansanin sojin saman Amurka na Ain al-Assad da ke lardin Anbar a yammacin Iraki a matsayin martani ga harin na Amurka da a yayinsa Janar din gami da wadanda ke tare da shi sukayi shahada.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*