?>

Wata Kotun Masar Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan ‘Yan Uwa Musulmi 24

Wata Kotun Masar Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan ‘Yan Uwa Musulmi 24

Wata kotu a birnin Damanhour dake arewacin kasar Masar, ta yanke hukuncin kisa kan wasu mambobin kungiyar ‘yan uwa musulmi su 24 bisa zarginsu da kisan ‘yan sanda.

ABNA24 : Laifukan da ake tuhumarsu sun hada da kai wani harin bam kan wata motar bus ta ‘yan sanda a lardin Beheira a cikin shekarar 2015, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan sanda uku, sai kuma wani dan sanda a shekarar 2014.

Wata majiyar shari’a ta bayyana cewa mutanen na da damar daukaka kara.

A kasar Masar dai ana aiwatar da hukuncin kisa ne kan fararen hula ta hanyar rataya.

A shekarar 2013 ne ma’aikatar shari’ar Masar ta ayyana kungiyar ‘yan uawa musulmi ta tsohon shugaban kasar mirigayi Muhamad Morsi a matsayin ta ‘yan ta’adda.

A Masar an bayyan cewa Tun bayan juyin mulkin da shugaba Abdel Fattah al-Sissi, ya yi a shakrar 2013, inda ya hambarar da mulkin Muhamad Morsi, yake daukan mataki mai tsauri na murkushe ‘yan hammayarsa.

Ko a bana kungiyar kare hakkin dan adam ta kasa da kasa Amnesty International, ta ce an samu karuwar aiwatar da hukuncin kisa a kasar ta Masar, inda adadin ya linka har sau uku, wanda daga 32 a shekarar 2019 zuwa 107 a bara.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*