?>

Venezuela:MDD Ta Bukaci A Daukewa Kasar Venezuela Takunkuman Tattalin Arziki

Venezuela:MDD Ta Bukaci A Daukewa Kasar Venezuela Takunkuman Tattalin Arziki

Manzon MDD zuwa kasar Venezuela ta bukaci a daukewa kasar Venezuela takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata. Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Alena Douhan ta na fadar haka bayan ziyarar aiki na kwanaki 12 da ta kai kasar. Douhan ta kara da cewa takunkuman tattalin arzikin sun yi mummunan tasiri a kan rayuwar miliyoyin mutanen kasar.

ABNA24 : Labarin ya kara da cewa a shekara 2019 ne gwamnatin Amurkan da ta shude ta dorawa kamfanin man fetur na kasar ta Venezuela takunkumin, sannan ta kwace kadarorin kasar Amurka ta mikawa ‘yan hamayyar kasar karkashin jagorancin Joar Guaido.

Banda haka kasashen turai ma sun dorawa kan ta Venezuela takunkuman tattalin arziki sannan sun hana ta taba kadarorinta da suke kasashen Burtaniya da Potigal.

Amma ‘yan adawar kasar ta Venezuela sun maida martani ga wannan bukatar ta MDD, inda suka bayyanan cewa mummunan halin da kasar Venezuela take ciki bai da dangantaka da takunkuman tattalin da aka dorawa kasar, sai da mummunan siyasar shugaban kasar Nicolas Madoro ne ya jefa mutanen kasar a cikin wahalar da suke ciki.

Kasashen Amurka da Turai sun ki amincewa sakamakon zaben shugaban kasan wanda aka gudanar a kasar ta Venezuela a shekarab 2018, wanda kuma shugaba Madoro ya lashe da babban rinjaye.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni