?>

Tunisia: Jam’iyyar EnNahdha Ta Bukaci A Daina Tada Jijiyoyin Wuya Dangane Da Rufe Majalisar Dokoki

Tunisia: Jam’iyyar EnNahdha Ta Bukaci A Daina Tada Jijiyoyin Wuya Dangane Da Rufe Majalisar Dokoki

Jam’iyyar siyasa mafi karfi a majalisar dokokin kasar Tunisia da aka dakatar, ta yi kira ga mabiyanta da su kwantar da hankalinsu su kuma daina zanga-zanga, don jam’iyyar ta zabi hanyar tattaunawa da fahintar juna da shugaba Kais Saeed kan matakin da ya dauka na dakatar da majalisar dokokin kasar da kuma tube firai ministan a ranar Lahadin da ta gabata.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa, Sauran jam’iyyu siyasa na kasar, sun bukaci shugaba Saeed ya bayyana tsarin da yake son bi, don dawo da democradiyya a kasar.

A ranar Lahadi da ta gabata ce shugaba Kais Sa’id na kasar Tunisia, tare da goyon bayan sojojin kasar ya dakatar da majalisar dokokin kasar, sannan ya tube firai ministn kasar ya kuma kori wasu ministocinsa tare da shi.

Shugabn ya dauki wannan matakin ne saboda rikicin da yaki ci yaki cinyawa a tsakanin shuwagannin siyasar kasar har ya kai ga wasu ma’aikatun gwamnatin kasar suka daina aiki.

Wannan yana faruwa ne a dai-dai lokacinda mutanen kasar suke fama da mummunan matsalolin tattalin arziki da kuma yaduwar cutar korona.

Yan kasar ta Tunisia da dama sun yabawa shugaban kasar kan matakan da ya dauka, sun kuma fito zanga zangar goyon bayansa a ranar litinin da ta gabata.

Shugaban ya kare matakan da ya dauka da kundin tsarin mulkin kasar wanda ya bashi damar daukar irin wannan matakin a duk lokacinda kasar ta shiga halin ka-ka-ni-ka-yi.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*