?>

Tunisia: Jam’iyyar Ennahda Ta Yi Burus Da Dokar Hana Zanga Zanga A Kasar

Tunisia: Jam’iyyar Ennahda Ta Yi Burus Da Dokar Hana Zanga Zanga A Kasar

Jam’iyyar Ennahda wacce take adawa da abinda ta kira mulkin kama karya na shugaba Kais Saeed ta ke yi, ta yi kira ga magoya bayanta su fito zanga zanga a gobe jumma’a don sabawa umurnin shugaban kasar na hana tarurruka har na makonni biyu don hana yaduwar Cutar Covid 19 a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kafin haka dai gwamnatin shugaba Kais Saeed ta bukaci ‘yan Tunusia su zauna a gidajensu na tsawon makonni biyu, sannan su rage tafiye-tafiye zuwa kasashen waje don bawa gwamnatin kasar damar yaki da cutar ta Covid 19.

Kungiyar Ennahda dai tana ganin karya dokar wata dama ce ta nuna rashin amincewa da mulkin kama karya na shugaban Kais Saeed, wanda yake mulkin kasar ba tare da amfani da kundin tsarin mulkin kasar ba, musamman bayan da ya rusa zabebbiyar majalisar dokokin kasar a shekarar da ta gabata.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*