?>

Tunisia : An Bai Wa Sojoji Umarnin Sanya Ido Kan Sha’anin Yaki Da Annobar Korona

Tunisia : An Bai Wa Sojoji Umarnin Sanya Ido Kan Sha’anin Yaki Da Annobar Korona

Shugaba Kaïs Saïed, na Tunisia, ya baiwa sojojin kasar umarnin sanya ido a sha’anin yaki da annobar korona a kasar.

ABNA24 : Matakin ya hada da sanya ido kan yadda ake aiwatar da sha’anin riga kafin cutar a fadin kasar da kuma adana riga kafin cutar.

Haka kuma sojojin zasu rika ba wa shugaban kasar shawar da kuma bada rahoto a ko wanne mako kan yadda ake tafiyar da aikin.

An dau wannan matakin ne a daidai lokacin da al’amuran da suka shafi sha’anin kiwon lafiya a kasar suka tabarbare, musamman kan batun yaki da annobar korona.

Tunisia tana sahun gaba a kasashen AFrika inda cutar korona ta fi wa illah.

A Tunisiar dai har yanzu ana jiran nadin da shugaban kasar zai yi na sabon firaminista, bayan da ya kori, Hichem Mechichi, a ranar Lahadi data gabata.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*