?>

Tawagogin Iran Da Rasha A Tattaunawar Vienna Sun Yi Ganawa Mai Tsawo

Tawagogin Iran Da Rasha A Tattaunawar Vienna Sun Yi Ganawa Mai Tsawo

Tawagogin kasashen Iran da Rasha da suke halartar tattaunawar da ke gunada kan batun shirin Iran na nukiliya, sun yi wata ganawa mai tsawo a yau a Vienna.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, a yau Asabar tawagogin kasashen Iran da Rasha da suke halartar tattaunawar da ke gudana kan batun shirin Iran na nukiliya, sun yi wata ganawa mai tsawo yau a birnin Vienna na kasar Austria, domin daukar mataki guda a tsakaninsu kan wasu batutuwa da suka shafi tattaunawar kan shirin Iran na nukiliya.

A yayin gnawar, shugabannin tawagogin na Iran Sayyid Abbas Araqchi, da kuma na Rasha Mikhail Ulyanov, sun kwashe tsawon sa’oi a yau suna ganawa, inda suka tattaunawa batutuwa da dama, domin daukar matsaya guda a kansu tsakanin Rasha da Iran.

Shugaban tawagar kasar ta Rasha Mikhail Ulyanov ya ce dole ne Amurka ta dauke dukkanin takunkuman da ta dorawa Iran da suke da alaka da batun shirinta na nukiliya.

Ya ce matakan da Iran ta dauka daga bisani dangane da jingine yin aiki da wasu bangarorin yarjejeniyar nukiliya bai sabawa yarjejeniyar ba, kuma idan Amurka ta aiwatar da hakan zai ba ta damar dawowa cikin yarjejeniyar ba tare da wata matsala ba.

Dukkanin bangarorin biyu sun bayyana tattaunawa da ake yi a halin yanzu da cewa tana yin armashi, kuma akwai yiwuwar a cimma matsaya ta karshe nan da ‘yan makonni masu zuwa.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*