?>

Taron Addu'oin Laylat Al-Raghaib A Masallacin Hagia Sophia A Istanbul Turkiya

Taron Addu'oin Laylat Al-Raghaib A Masallacin Hagia Sophia A Istanbul Turkiya

Tehran (IQNA) a daren jiya ne aka gudanar da tarukan addu'oi domin raya daren Laylat Al-Raghaib daren Juma'a na farko a cikin watan Rajab.

ABNA24 : Bisa ga rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, a daren jiya an gudanar da taron addu'oi domin raya daren Laylat Al-Raghaib, daren Juma'a na farko a cikin watan Rajab a masallacin Hagia Sophia da ke birnin Istanbul a kasar Turkiya.

Wannan zaman addu'oi ya samu halartar malamai da dubban musulmi, wanda kuma shi ne karon farko da ake gudanar da irin wannan taro a cikinsa tun bayan da aka sake mayar da wurin ya koma masallaci.

Tun shekaru 1500 da suka gabata ne aka gina wannan wuri a matsayin babbar coci ta mabiya addinin kirista 'yan darikar Arthodox, amma bayan da sarakunan daular Usmaniya suka kwace iko da birnin Istanbul a shekara ta 1453, sun mayar da wurin ya koma masallaci.

Amma a shekara ta 1934 tsohon shugaban mulkin kama karya na Turkiya Kamal Ataturk ya mayar da wurin ya zama wani wurin tarihi, da masu yawon bude ido suke ziyarta, amma a cikin shekarar da ta gabata, shugaban Turkiya na yanzu Rajab Tayyib Erdogan ya sake mayar da wurin masallaci.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni